Kunya adon ‘ya mace: Ya abin ya ke a zamanin nan?

Daga SADIYA GARBA YAKASAI

Da fatan na same ku lafiya. Da farko yau zan fara miƙa godiyata ga dukkan masu yaba mun da nuna jin daɗinsu yadda suke gamsuwa da wannan fili namu mai albarka.

Muna godiya kuma muna jinjina wa masu bin mu sau da ƙafa.Yau za mu taɓo yadda rayuwar yaranmu mata take son canja salo daga kunya zuwa fitsara. A da ɗiya mace da kunya aka san ta ba a san ta da buɗe baki ba, duk matsi ta ce saurayi yayi mata kaya, ko ya ba ta kuɗi ba.

Subuhanallahi! ta yaya iyaye za su bar wannan koyi da iyayenmu suka yi mana na kawaici da kau da kai ya wargaje? uwa na ganin ‘yarta na tambayar namiji yayi mata abu ba kunya ba kawaici. Idan dai an bi ta ɓarawo, to a bi ta ma bi sawu ma. Gaskiya idan uwa ta yi wa ɗiyarta koyi da tarbiyya to ba za ta iya bin namiji ta ce ya ba ta kuɗi ba, ko ya yi mata wani abun.

Ita tarbiyya fa daga gida take farawa, daga gidan kuma daga uwa. Kafin mu je ga uba, Uwa ya kamata ta yi wa ɗiyarta tarbiyya ta nuna mata illar tambayar namiji kuɗi, daga nan tarbiyya da mutunci yake lalacewa.

Idan shi da kansa ya ɗauka ya baki, ki karɓa da godiya. Don ya fi mutunci ba roƙo ba. Shi fa roƙo karya daraja yake, ya kuma ɓata suna. Namiji nan da nan za ki sare masa ya ji sam ba ya ƙaunar ki, ko kuma ki fitar masa daga zuciya. Idan har na arziki ne, sai ya yi miki nuni da ki daina. Wani kuma idan ba na arziki ba ne, da wannan kwaɗayin naki zai yaudare ki. Ya ba ki kuɗin, ya kwashe miki mutunci, ya bar ki ba tsuntsu ba tarko.

Iyaye ku ya kamata ku nuna wa yarinya rashin kyautatawa a roƙo. Ko da macen aure ce ta fiye tambaye-tambaye ga miji, wallahi ƙosawa yake. Ko ya dinga mata gani-gani, idan ta yi sa’a, ya gaya mata dalili.

Abu na gaba, kyautata wa iyali babban aiki ne a gun iyaye. Muddin za ku kula da buƙatun yaranku, to da wuya su yi roƙo. Yanzu maza sun damu da wannan ɗanyen aiki da ‘yanmata ke yi na roƙo. Ya Allahu, ina kunyar da Allah ya ba mu ta mata?

Wani zai yi haƙurin ya ba ki. Amma ki sani, babu soyayyar da kike buƙata ko tunanin in kin je gidansa zai ba ki kuɗin. Maimamakon ya ba ki ma, gori za ki sha wallahi.

Yana da kyau iyaye su sa ido a kan rayuwar yaransu mata, tun daga waje suna son a ba su, ina kuma da an shiga gidan? Da kanmu ma muke saya wa yaran namu shiga wata rayuwar, wallahi.

Yana da kyau ma a soke anko da duk wata taɓargaza da za ta jawo masifa. Wani yaron bai da tunanin da za a ce masa ya haƙura, kuma ya haƙura ɗin.

Su ma mazan suna roƙon, sai ka ga namiji ya ce mace ta yi masa wasu buƙatun da sunan bashi, wai zai biya ta idan ya samu. Kawai ba zai fito ne ya ce roƙo yake ba. To me ya sa wai roƙon ya yi yawa ne a samartakar yanzu, mutuwar zuciya ko me?

Me ya sa mata suke cewa maza su yi musu abu? Shi fa roƙo abu ne mai nauyi a gurin mace. Amma na yanzu, ya fi komai sauƙi a gurinsu, wallahi. Ya kamata mu sa ido a kan yaranmu, ko ƙaƙa ne ya kamata iyaye mu dinga agaza wa yaranmu da buƙatunsu. Idan mun ba su kulawa, insha’Allahu za a samu sauƙi.

Matasanmu sun zama wasu iri. Muna ganin suna neman fin ƙarfinmu, ko ma sun fi. Ko ta ina iyaye za a ce, tunda su suka haife su, su kuma ya kamata su kula da tarbiyyarsu. To amma ga shi alamomi sun nuna cewa, iyayen irin taɓarar da yara suke da rashin kunya nema yake ya wuce gona da iri. Duniyar Soshiyal midiya za ku shiga, ku ga yadda yaranmu suka koma.

Satin nan aka yi abunda ya ɗaga wa kowa hankali. Yara ƙanana su fito duniya suna lalacewa. Yaro ya ce budurwa ta sumbace shi ba kunya ba tsoron Allah ta aikata, kuma ba tare da ta voye ma fuskarta ba a gaban duniya. Gwara shi namiji ne amma ita fa mace ce da aka santa da kamun kai, wa zai yi sha’awar aurenta a gaba ko tana da tabbacin shi ɗin son ta yake? Iyaye muna ina ne muka bar yara na wannan abun kunyar a duniya?

Ku  duba yaran nan ƙanana da aka nuno sun yi garkuwa da yaro ƙarami ɗan maƙocinsu, wai jari yake nema shi yasa ya yarda da abokin nasa suka sace yaron. Don Allah mu ga fa duk ba su wuce shekaru 15 zuwa 17 ba ta yaya za mu ji daɗi yaranmu sun ɗau ɗabi’a mara kyau? Dole mu dage mu daɗa sa ido fa a kan yaranmu don Allah abun nasu daɗa gaba yake.

Wasu ba za su yarda iyaye na yin iyawar su ba. Gani za a yi ma ba sa yi. To Wallahi wayon yaran yanzu ya wuce na iyayen ma. Mu sa ido kawai da wa suke mu’amala, mu dinga kuma jan su a jiki, da nuna musu mu ne iyaye, mu ne kuma ƙawayensu, insha’Allahu za a samu sauƙi. Duk wata jarabawa na tare da ƙalubale, dole sai mun yi haƙuri, mun ba wa yaranmu kulawa.

Lalacewar tarbiyya ta shafi kowa!
Wannan rayuwa da ake ciki ta shafi kowa da kowa, babu maganar ɗan wani ko ‘yar wani ta shafi kowa. Duk mai ɗa zai ji tsoron wannan rayuwa da muka tsinci kanmu a ciki. Sai mun yi da gaske, sannan za mu samu kan yaranmu da suka ɗau dala ba gammo, suka aza.

Taɓarɓarewar tarbiyya daɗa gaba take, yara masu shaye shaye sun ƙi karatu sai yawace-yawace. ‘yammata na ƙaryar su wasu ne, suna fita da samari guraren shaƙatawa ba kunya, kuma su koma gidan iyayensu ba tare da iyaye sun binciki yaransu ba. Yara ƙanana na shirya yadda za su samu kuɗi ta hanyar garkuwa, ko kashewa, wannan kaɗai ya ishe mu ishara da tashin hankali. Kullum muka kwanta muka tashi, sai mun tashi da labarai marasa daɗi har fargabar buɗe rediyo muke yi a yanzu.

Duk uwar da ta san ciwon ɗa, ta san muna cikin halin tashin hankali mara iyaka. Wallahi sai dai mu yi ta addu’a ga kanmu da yaranmu. Allah ya kawo mana ƙarshen waɗannan fitintinu, mu dage da yin addu’a, kuma ko ma samu sauƙin wasu abubuwan Allah ya sa mu dace.

Nan za mu tsaya, sai kuma a sati na gaba, Allah ba mu ikon gyarawa. Wassallam.