Rundunar ‘yan sanda ta amince jami’anta mata su sanya hijabi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sufeto-Janar na ‘Yan Sandan Nijeriya, IGP Usman Alƙali Baba ya amince jami’an ‘yan sanda mata Musulmi su fara sanya ɗan ƙaramin hijabi kan kayan sarki idan suna da sha’awar hakan kamar yadda sanarwar ta ce.

Sanarwar ta ce an amince jami’an ‘yan sandan mata su saka ƙaramin hijabi a cikin kakin da yin amfani da jakar hannu wadda hukumar ta amince da ita da kuma takalmin ‘yan sanda da shi ma aka yarje musu su yi amfani da shi.

Wanna shi ne karo na farko da jami’an ‘yan sanda mata suka samu wannan ‘yancin tun bayan kiraye-kiraye da ƙungiyoyin Musulmai suka dinga yi ga hukumar ‘yan sandan Nijeriya.

A wani labarin mai kama da wannan kuwa, Ƙungiyar Rajin Kare ‘Yancin Musulmai ta Ƙasa, MURIC, ta yaba wa Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda, Usman Alƙali Baba a bisa amincewa da amfani da hijabi ga ‘yan sanda mata a faɗin Nijeriya.

Shugaban MURIC, sashin Jihar Zamfara, Farfesa Ahmad Galadima, shi ya yi yabon a wata sanarwar da ya sanya wa hannu a yau Juma’a.

Ƙungiyar, a cikin sanarwar, ta bayyana cewa amincewar ta Sufeto-Janar wata babbar nasara ce.

MURIC ta ƙara da cewa wannan matakin na Sufeto-Janar zai ƙara martaba da darajar Rundunar ‘Yan Sanda a idon al’umma.

Ƙungiyar ta gode wa Rundunar ‘Yan Sanda, musamman Sufeto-Janar, a bisa amincewa da amfani da hijabi ga ‘yan sanda mata, bayan sauraron koken da Musulmai su ka yi.

Ta ƙara da cewa wannan amincewar ta sanya za a kalli Rundunar ‘Yan Sanda ta Ƙasa a matsayin wacce take bin tsarin aikin ɗan sanda na duniya.

“Saboda haka mu na bai wa masu baki da kunu shawara da su ɗauka cewa wannan matakin wani sabon salo ne a yaƙi da ‘yancin ɗan adam,” inji sanarwar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *