Kotu ta ba da umarnin a saki matar wanda ya kashe Hanifa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wata babbar kotu da ke zamanta a Kano ta ba da umarnin a saki matar wanda ake zargi da kashe wata ’yar shekara 5, Hanifa Abubakar, da kuma binne ta a harabar makarantar da ya ke shugabanci.

Matar, wacce aka zarga da haɗa baki da mijinta wajen yin garkuwa da kuma kashe ƙaramar yarinyar, an sako ta ne a ranar Juma’a.

Jamila dai ta bayyana cewa, ba ta da wani laifi a lokacin da ta gabatar da shaida kan mijinta a wata babbar kotun Kano a ranar Alhamis.

Tun da farko lauyan gwamnati Barista Lamido Soron Dinki ya roƙi kotun da ta duba shaidar da matar ta bayar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *