Ukraine da Rasha sun yi zama na biyu don tsagaita wuta

Duk da zaman da zama na biyu da wakilan Ukraine suka yi da Rasha don tattaunawa da zummar cimma matsaya kan tsagaita musayar wuta tsakanin ɓangarorin biyu.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi amanna cewa, rikicin Ukraine zai yi mummunan ƙazancewa nan gaba, bayan wata ganawa da ya yi ta tsawon mintina 90 da takwaransa na Rasha Vladimir Putin, wanda alamu ke nuna cewa, manufarsa ita ce, mamaye Ukraine baki ɗayanta.

Ɗaya daga cikin makusantan Shugaba Macron da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce,  a yayin tattaunawar, Shugaba Putin ya jaddada aniyarsa ta ganin ya kakkaɓe aƙidar ‘yan Nazi daga zukatan ‘yan Ukraine kuma ya haƙiƙance cewa, akan gaskiyarsa yake ƙaddamar da farmaki.

Rahotannin baya-bayan nan na cewa, sojojin na Rasha sun yi wa Kharkiv, birni na biyu mafi girma a Ukraine luguden wuta, abin da masu shigar da ƙara na Majalisar Ɗinkin Duniya ke bincike a kai saboda yiwuwar aikata laifukan yaƙi.

Kazalika, sojojin na Rasha sun yi ruwan wuta kan birnin Mariupol mai tashar jiragen ruwa, yayin da suka karɓe iko da birnin Kherson da ke kusa da gabar tekun Black Sea a kudancin Ukraine.

A ɓangare guda, Faransa ta ce, ta ƙwace wani katafaren jirgin ruwa mallakin wani babban jami’in gwamnatin Rasha mai kusanci da shugaba Vladimir Putin wato, Igor Sechin.

Faransa ta ƙwace jirgin ruwan ne a gaɓar ruwan Riviera sakamakon takunkuman da Ƙungiyar Tarayyar Turai ta ƙaƙaba wa Rasha.