Kotu ta rufe asusun ajiyar ƙananan hukumomin Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta rufe asusun bankin ajiyar haɗaka ƙananan hukumomin jihar Katsina sakamakon ƙin bin umarninta da gwamnatin jihar ta yi, inda tun farko kotun ta umarci gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Aminu Bello Masari akan ta biya shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli da gwamnatin ta rushe a shekara ta 2015.

Shugaban jam’iyyar adawa a jihar ta PDP wato Hon. Yusuf Salisu Majigiri ne ya bayyana hakan a sakatariyar jami’iyyar da ke birnin Katsina a lokacin da yake yi wa ɗaruruwan magoya bayan jam’iyyar da ‘yan takarar shugabannin ƙananan hukumomi na jam’iyyar jawabi a zaɓen ƙananan hukumomi da za a gudanar a jihar cikin watan Afrilu na wannan shekarar.

Majigiri ya ƙara da cewa mai Shari’a Emeka Nwite ne ya yanke hukuncin a zaman kotun da aka yi a watan Fabrairu a ƙarar mai lamba FHC/Abuja/CS/122/2022.

Wannan hukunci na rufe asusun haɗaka ƙananan hukumomin zai ci gaba da aiki har zuwa ranar 21 ga watan Maris, 2022.

 Da yake mayar da martani akan hukuncin, shugaban jam’iyyar APC mai mulkin jihar Alhaji Muhammad Sani ya bayyana cewar gwamnatin jihar Katsina ta biya haƙƙoƙin dukkan tsofaffin shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli na jihar kamar yadda kotun ƙoli ta bada umarni tun farko, inda ya ƙara da cewa za su gabatar wa babbar kotun tarayyar da shaidar hakan a zama na gaba.

Idan dai za a iya tunawa gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Aminu Bello Masari ta rushe dukkan zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomin jihar 34 da kansiloli a shekara ta 2015 lokacin da Gwamna Masari ya kama aiki a matsayin gwamnan jihar bisa zargin shugabannin ƙananan hukumomin da aikata ba daidai ba, sai dai shugabannin ƙananan hukumomin na jam’iyyar PDP sun kai gwamnatin jihar ƙara inda suka yi nasara domin kuwa kotun ƙoli ta umarci gwamnatin jihar da ta biya su dukkan haƙƙoƙinsu tun daga ranar da aka kore su har zuwa lokacin da wa’adin mulkin su zai ƙare.