Ruwan jiki

Daga MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI

Yan uwa masu karatu Assalamu alaikum. Barkanmu da wannan lokaci, barkan mu da sake saduwa a wannan shafi mai ilmintarwa, da ke zayyano muku bayanai game da duniyar jikin ɗan adam, domin ku fa’idantu kuma ku ilmintu, kuma ku san yadda jikinku ke aiki. 

A cikin Littafi mai Girma,  Sarkin halitta ya faɗa cewa: “Kuma Mun sanya duk wani abu rayayye ya zamto daga ruwa”. Ubangiji Ya yi gaskiya.  Idan ka yi wa duk halitta mai rai kallon tsanaki, za ka tabbatar da cewa akwai ruwan a tattare da ita. Sawa’un tsirrari ne ko kuma dabbobi. Yanzu dai ba zan vata lokaci wajen kawo muku bayanai akan yadda ruwan jikin sauran halittu yake ba, zai mayar da hankali ne akan ruwan jikin ɗan Adam, kamar yadda yake a maƙasudin wannan shafi.

Malam Bahaushe ya na cewa: “ruwa abokin aiki”. A cikin jikin ɗan Adam ma, haka abin ya ke. Mafi yawan sashen jikin ɗan Adam duk ruwa ne. Amma idan nace ruwa ba ina nufin ruwa da muka Saba gani ba; shi wannan ruwa ne  na musamman mai ɗauke da narkakkun sinadarai kala-kala waɗanda ke tabbatar da daidaituwar ayyukan jikin bil adama.

Masana sunce kaso sittin bisa ɗari na jikin ɗan Adam duk ruwan jiki ne, sauran sashen kuma kaso arba’in. Rayuwar ɗan adam kacokan ta ta’allaƙa ne akan wannan ruwa da sinadaran da ke cikinsa. Saboda haka samuwar duk wani sauyin da ba a buƙata a cikin yawan ruwan jiki kan iya haufarwa da mutum matsala.

Kafin nayi nisa, ta kamata na yi bayanin muhalli ko bigiren da wannan ruwa ya ke. A rubuce-rubucen da suka shuɗe, na yi bayanin yadda ƙwayar halittar jikin ɗan Adam ta ke. Saboda ƙanƙantarta, ido ba ya iya ganinka, amma na’urar nazarin siffar halittu wato “microscope” ta na iya ƙara girman ƙwayar halitta ta yadda idan mutum misali ɗalibin kimiyya ya shiga cikin ɗakain gwaje-gwaje, zai iya nazari akan ƙwayar halittar da abinda ke cikinsa ta hanyar gin amfani da waccan na’ura.

To a cikin kowacce ƙwayar halitta ta jiki akwai ruwa; haka ma a kewaye da ita, akwai ruwa. Kenan za mu iya cewa kowacce ƙwayar halittar jiki ta ɗan Adam cike take da ruwa, kuma tana wanka a cikin ruwan jiki. Misalin yadda abin yake shi ne kamar a zuba tsabar gero cikin wani mazubi mai ɗauke da ruwa, a yi ta zuba geron har sai ya kawo kusa da inda ruwan ya ke. Wannan shi ne misalin yadda ƙwayoyin halittu suke a tsullum a cikin ruwan jiki.

Kuma kar ki manta, da za mu duba dakyau, za mu ga cewa kowacce ƙwayar tsabar gero tana kusa da wasu ne, ma’ana tana maƙwabtaka da sauran tsabar da ke kusa da ita. To kamar haka ne a jikin mutum: ƙwayar halitta ɗaya ta na maƙwabtaka da sauran da ke gefe-da-gefenta. Haƙiƙa juma akwai musayar saƙonni da ke wakana a tsakaninsu.

Ya kamata in yi wannan bayanin tun da na tavo ƙwayar halitta. A jikin ɗan Adam, akwai ƙwayoyin halittu iri iri, ba kala daya ne ba! Bari na baku misali: akwai ƙwayoyin halittar jini (Farare da jajaye); akwai ƙwayoyin halittar ƙwaƙwalwa, akwai ƙwayoyin halittar ƙashi; akwai ƙwayoyin halittar tsokar nama; akwai ƙwayoyin halittar fata; da sauransu. Kowacce daga cikin waɗannan da na lissafo na da tsarin aiki, siffa, bigire, adadin rayuwa, da kevance-keɓancenta. Kuma kowacce na ɗauke da ruwan jiki daidai da irin aikin da take gudanarwa a jikin ɗan adam.

Kamar yadda na faɗa a baya, a kaso ɗari na jikin mutum, kaso sittin bisa ɗari na ɗauke da ruwa ne. A ilimin likitanci, ana amfani da nauyin mutum da ya kai kilogram Saba’in a ma’aunin gwada nauyi. Wato mutum me nauyin kilogram Saba’in shi ne abin kwatance a ilimin likitanci. Idan mu ka ce kaso sittin sau nauyin mutumin (60 bisa 100 sau 70), za mu samu lita 42 ta ruwan jiki.

A cikin lita arba’in da biyunnan, lita ishirin da takwas shi ne jumullar ruwan da ke cikin ƙwayoyin halittu, ragowar lita goma sha huɗu shi ne ruwan jikin da ƙwayoyin halittun ke wanka a ciki.

Na ce akwai ruwa a cikin kowacce ƙwayar halitta, kamar yadda akwai ruwa a kewaye da ita. Sinadaran da ke cikin ƙwayar halitta kan fito daga cikinta su dawo cikin ruwan da ke kewaye da ita,  hakazalika sinadaran da ke cikin ruwan da ke kewaye da ƙwayoyin halittu kan sauya sheƙa su koma cikin ƙwayoyin halittu. Ya danganta da buƙatar jiki a daidai wannan lokaci.

Kafin na faɗi irin ayyukan da ruwan jiki ya ke yi a jikin bil adama,  zan so na ƙarashe bayanin guraren da ruwan jiki ya ke. Idanun ɗan Adam cike yake da ruwa. Bakin ɗan Adam kullum cikin zubo da yawu yake. Yawu wani farin ruwa ne tsinkakke da kuttun zubo da yawu ke fesowa kowacce Rana. Kaɗan daga cikin ayyukansa  su ne: shi ne ruwanda ke dansasa bakli, ya wanke ƙwayoyin cuta irinsu bakteriya, ya taimaka wajen jiƙa sandararren abinci; ya taimaka wajen tauna,  ya taimaka wajen jeranta kalmomi yayin magana.  Ku jira rubutu akan harshe domin ƙarin bayani.

A cikin ƙoƙon kai, akwai wani ruwa wanda ƙwaƙwalwar mutum ke wanka a ciki. Kamar dai yadda za ka sanya abu mai ɗan nauyi a kan ruwa ta dinga yawo ba tare da ya nurse bam to haka itama ƙwaƙwalwa.  Sai dai ita ƙwaƙwalwa a Katange ta ke cikin ƙoƙon kai. Saboda haka ta na da iyaka wajen kai-kawo, wato daga ɓangaren hagu zuwa na dama. A cikin wannan ruwa akwai sinadaran da ke bawa ƙwaƙwalwa abinci.

Wasu masana sun ce wannan ruwa yana sabunta zagayawarsa a kewayen ƙwaƙwalwa kullum sau biyar. Su ka ce wannan ya na nuni da cewa itama ƙwaƙwalwar ɗan Adam na alwala sau biyar kowacce Rana. Sannan su ƙara da cewa sashen ƙwaƙwalwar mutum na gaba, wato ɓangaren goshi ya ɗan tuntsira; wannan shi yake nuni da cewa ƙwaƙwalwa ita ma ta yi wa Sarkin Halitta sujjada! Allahu Akbar!

Akwai ruwa a gavvai na ɗan Adam ko kuma in ce mahaɗar ƙashi. Amfanin wannan ruwa shi ne hana siƙewar mahaɗar ƙashi guda biyu da ke gugar juna, abinda a turance ake Kira da “friction”.a siffa, wannan ruwan yana yanayi da ruwan ɗanyen ƙwai.  Yayin da shekaru su ka ja,  tsufa ya fara kawo hari, yawan wannan ruwa na raguwa, Wanda hakan kan iya sanya kaushin mahaɗar ƙashi, daga nan kuwa sai tafiya ta fara zama jidali!

Masu karatu ku tara a sati mai zuwa domin ci gaba da kawo muku bayanai akan jikin ɗan Adam. Kafin nan na ke cewa Assalamu alaikum.