Asalin Zariya da Masarautar Zazzau

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Zazzau suna ne da ya samo asali daga sunan takobi wanda kuma daga baya ya koma sunan wata babbar masarauta mai daɗaɗɗen tarihi daga cikin masarautun Arewancin Nijeriya. Ɗalhatu (2002), ya kawo cewa, duk wanda ke riƙe da wannan takobi to shi ne sarki, sannan kuma su na kiran sa da sunan ‘Maɗau Zazzau’, ma’ana, wanda ke ɗauke da Zazzau.

Ya zo a Bryant (shekarar bugu ta goge), cewa, shi wannan takobi mai suna Zazzau, abu ne da jama’ar wasu yankuna na masarautar Zazzau ɗin ke girmamawa, rantsuwa ma idan za su yi da shi suke yi. Wasu kan ce, tushen wannan kalma ta ‘Zazzau’ yana da rassa biyu, na farko yana da nasaba da yanayin ƙasar ta Zazzau, wanda daga Katsinanci ke nufin ‘zo-zo’, wato ƙasa mai laka, ba mai rairayi ba, wadda za a iya yin shuka a kanta, kuma ta tsiro.

Asalin kalmar Zariya:
Zariya kalma ce da ta samo asali daga sunan Zariya ‘yar Sarki Bakwa Turunku, wadda ƙanwa ce ga Sarauniya Amina.

Bambancin Zazzau da Zariya:
Zazzau masarauta ce, wadda ta ƙunshi dukkan ƙasashe da garuruwan da ke bin masarautar. Zariya kuwa shi ne babban birnin da sarki yake zaune da hakimai da ’yan majalisarsa ana gudanar da mulki. Sauran hakimai da suke da ƙasashe suna kawo wa sarki rahoto, su kuma ana aika masu da umarni.

Kafuwar Masarautar Zazzau:
A zamanin maguzanci, wato shekaru aru-aru da suka gabata, babu wani addini da ya shigo, sai al’adu ko rayuwa irin ta maguzanci. Kuma ƙaura daga wannan waje, a koma wancan waje, ita ce al’adar Bil’Adama, a qoqarin neman wajen da zai zauna ya sami ingatacciyar rayuwa. Mafi yawan ayyukan da jama’a kan yi a lokacin su ne, noma da kiwo. Wannan lokaci ne kuma masana tarihi ke kira zamanin ‘Zo-zo’, wato zamanin maguzanci, wanda ya kasance tun kafin shigowar addinin Musulunci.

Lokacin da al’umma suka riƙa taruwa, suna samun shugabanci, har sarakunan Have suka fara mulki, aka samu kafuwar Hausa Bakwai, wato zuri’ar Bayajidda da Sarauniya Daurama.
Kuma Zazzau na ɗaya daga cikin ƙasashen da aka ba ’ya’yan Bayajida mulki.

Bayanin da aka samo daga bakin Marigayi Malam Habibu Na-Turunku, wani uban gari na Turunku, ya nuna cewa, Gunguma shi ne sarkin Zazzau na farko, kuma ya yi tafiyayya ne daga Daura, ya bi ta Kano da Rano, kuma ya fara yada zango a Kangi.

Waɗanda suka biyo bayansa sun kafa biranen mulkinsu ne a Kawari da Rikocci da Wuciciri da kuma Turunku, kafin su je Zariya.

Nohir ta auri wani baƙo, ta haifa masa da namiji, kuma aka sa wa ɗan suna ɗan Bakwa Turunku. Daga baya sunansa ya koma Bakwa Turunku, wanda ya gaji sarautar kawunsa Kawanissa a shekarar 1536.

Bakwa Turunku ya yi sarauta ne a garin Turunku, kuma har yanzu akwai sauran kufan masarautar ta Turunku a can ƙasan tsaunukan da suke shimfiɗe a yankin gabashin Zariya.

Kafuwar Birnin Zariya:
Kamar yadda aka sami labari daga wajen Marigayi Malam Habibu Na-Turunku, wani uban gari na Turunku, ya nuna cewa, Zariya ‘yar Bakwa Turunku, kuma ƙanwar Sarauniya Amina ce ta kafa birnin Zariya, don haka ake kiran birnin da sunanta.

Hakan kuwa ya biyo bayan yadda hedikwatar mulki ta Zazzau ta yi ta sauya wuri saboda matsalar rashin ruwa, a zamanin mulkin Bakwa Turunku, wato mahaifin Sarauniya Amina da Zariya. Hedikwatar ta tashi daga Bomo zuwa Wucicciri zuwa Ancau zuwa Kargi, ta koma Turunku. A wancan lokaci an ce sai Bakwa ya ga Turunku ta yi wa mutanensa kaɗan a matsayin hedikwatar mulki, ga matsalar ruwa ana fama da ita. Saboda haka, sai ya koma Zariya a shekarar 1537.  Daga nan ne kuma masarautar Zazzau ta koma Zariya.

Amma ba a shiga Zariya kai tsaye ba, sai Bakwa Turunku ya gaya wa ‘yarsa Zariya, cewa ta je wajen kufannin iyayensu, wato Kufena kenan, ta je ta fara zama a wurin, kuma akwai rafi a wajen. Sai dai da Sarauniya Amina, wadda ita ce ‘ya a wajen Zariya, ta dawo daga yaƙe-yaƙenta, sai ta ce wurin ya yi faɗi da yawa. Idan aka gina hedikwatar mulki a wurin a wancan zamani na yaƙe-yaƙe, to mahara za su iya kai masu hari. Saboda haka, ta ce a koma kusa da rafin da ake kira Fadamar Bono a cikin gari, wanda daga baya da Fulani suka karɓi mulki suka mayar da sunan zuwa Fadamar Sarki.

Da aka gama sake shata gari, sai Sarauniya Amina ta sa wa wannan zagayen da’irar da aka yi sunan ƙanwarta, wato Zariya.  Don ta girmama sunan ‘yar uwarta, kuma dalilin sunan garin Zariya kenan. Kuma ta gina gida a cikin gari, inda ya zama fadar Zazzau, inda mahaifinta ya zauna, kuma har yanzu nan ne fadar masarautar Zazzau.  Ana kiran gidan da sunan ‘Gidan Bakwa’.

Asalin Ganuwar Zazzau:
A zamanin da, mai ƙarfi shi ke da iko a ƙasashen Hausa da sauran wurare, saboda haka kowacce ƙungiyar al’umma da suke so su yi ƙarfi, sai sun kewaye kansu, yadda mahara ba za su shigo masu ba. Wannan shi ne dalilin ganuwa a ƙasar Hausa, kuma inda duk aka yi ta, an yi ne don wurin ya zama hedikwatar mulki na al’ummar wajen.

To, a Zazzau waɗanda suka fara yin ganuwa a cikin gari, aka mayar da cikin gari hedikwata, wato babban birnin mulki na Zazzau, su Bako Turunku ne, mahaifin Sarauniya Amina ta Zariya. 

Ganuwar Zariya, ita ce ta ɗauka tun daga dutsen Kufena, ta kewaya zuwa Hanwa, ta shigo wajen barikin soja, inda ake kira Jushin Waje. Ta biyo ta Ƙofar Galadima, ta Ƙofar Kona, ta haɗa da rafin Saye, sannan ta koma ta Gwargwaje, ta haɗu da Wusasa, kana ta koma Kufena. Saboda sanin dabarun yaƙi, sai Sarauniya ta sa bawanta, wato Bono, ya je ya sara da’ira da rafin Sarki a tsakiya ya kewaya aka yi ƙofofin garin guda takwas, waɗanda suka haɗa da Ƙofar Kibo, da Ƙofar Kona da Ƙofar Galadima, da Ƙofar Bai, da Ƙofar Doka wadda a da ake kira Ƙofar Kano, da Ƙofar Jatau, da Ƙofar Kuyambana da kuma Ƙofar Gayan.

Sarauniya Amina:
Sarauniya Amina Have ce ta Zazzau, sai dai wasu masana tarihi na kallon ta a matsayin Sarauniya, amma ba Sarki ba ce, don haka babu sunanta a jerin sarakunan Have. Ma’ana, akwai sarautu da ake ba ’ya’ya mata a da a ƙarƙashin sarautar Have. Alal misali, akwai Sarauniya, akwai Gimbiya, akwai Iya, akwai Madanni, da dai sauran su. Duk waɗannan sarautu ne na ’ya’yan sarakunan Have. Saboda haka, Sarauniya Amina ba wai ta zama ita ce Sarki ba, a lokacin mahaifinta (Bakwa Turunku) yana sarki, ita kuma tana matsayin sarauniya, wato babbar ’yar sarki. Bisa al’ada, babban ɗan sarki shi ne shugaban rundunar sojoji na wannan masarauta.

To, ita Amina ita ke riƙe da wannan kambi, kuma ita ta yi ta yaƙe-yaƙe. Ta buga daga Zazzau ta yi arewa har Kano, har Katsina, ta kare iyakokin masarautar Zazzau.

Ta yi kudu da yamma, don ƙara faɗin ƙasa da ƙarfin mulki, kuma da haka ne ta dangana da ƙasar Neja ta yanzu, ta dangana da ƙasar Idah, wato ƙasar Attah Gara a jihar Kogi.

Ta je har ƙasar Nasarawa ta yau, saboda ƙarfin yaƙi da iya gudanar da yaƙi da jaruntaka. Tana da rundunoni da take jagoranta, kuma duk inda suka tunkara suna yin nasara, kamar yadda tarihi ya nuna.

Yadda aka sami gidaje huɗu na Sarautar Zazzau:
Idan sarautar Zazzau ya kasu huɗu ne, saboda Zazzau ƙasa ce wadda ta tattara ɗimbin al’umma da suka fito daga wurare daban-daban, don neman ilimin addinin Musulunci.
Saboda haka, a lokacin da jihadin Shehu Usman Ɗanfodiyo ya zo, an sami malamai ne masana ilimin addinin Musulunci, da shari’o’i, da kuma ƙa’idar mulki na Musulunci.

A lokaci ba wai ana la’akari ne da cewa wane ya gada ko wane ne ya gada ba, ana neman wanda zai zama khalifa, don tabbatar da kafuwar addinin Musulunci a Zazzau.

Zazzau wata cibiya ce, tun ma kafin jihadin Shehu Usman Ɗanfodiyo, saboda kasancewarta ‘Zo-zo’, ƙasa mai albarka, mai ɗaukar komai da komai na noma, tana da laima da ni’ima. Kowa yana son ya je ya zauna a Zazzau, ya amfana ta fuskar noma da kiwo.

Wannan ya sa Fulani da yawa suka zauna a Zazzau tun zamanin mulkin Have, kuma da yawansu abin da suke yi baya ga kiwo, shi ne karatun addini. Kuma lokacin da ɗan uwansu Shehu Usman Ɗanfodiyo ya ɓullo, sun kai masa gaisuwar caffa, suka yi masa mubayi’a, ya yarda da su. Suka zauna da shi, suka yi karatu tare da shi, suka yi yaƙe-yaƙen da aka yi tsakanin Sarkin Gobir da Usman Ɗanfodiyo.
Tun kafin a yi ganuwa, akwai mutane, wato Fulani, irin su Malam Musa da Yamusa da Malam AbdulKarim da su AbdulSalam da ke zaune a cikin garin Zariya, suna koyarwa ta addinin Musulunci.

Da suka ji ɓullowar Shehu Usman Ɗanfodiyo yana zuwa wurare daban-daban yana kira da a gyara addinin Musulunci, suka yadda da abin da yake yi, suka yi masa mubaya’a.

Tarihi ma ya nuna cewa, Malam AbdulKarim ya zauna da Shehu Usman Ɗan Fodiyo, ya yi karatu a wajensa. Shi kuwa Malam Musa kusan tsaran Shehu Mujaddadi ne, kuma tare suke tafiye-tafiye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *