Sabon Ministan Ilimi ya janye dokar shekara 18 ga masu neman gurbin karatu a manyan makarantu

Sabon Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya soke ƙa’idar shekaru 18 a matsayin mafi ƙarancin shekaru don samun shiga manyan makarantu a Nijeriya.

Dr. Alausa ya bayyana haka ne a yayin taron manema labarai na farko da ya gudanar a yau Talata, a Abuja.

Sai dai Ministan ya bayyana cewa babu shirin sake duba hukuncin da gwamnatin tarayya ta yanke na ƙin amincewa da takardun shaidar digiri sama da 22,700 da wasu ‘yan Nijeriya suka samu daga wasu “makarantu na bogi” a ƙasashen Togo da Jamhuriyar Benin.