Daga SALMANU FARIS ADAMU KUDAN
Tsokaci:
Littafin ‘Rayuwar Bilkisu’, littafi ne, wanda Ayuba Muhammad ɗanzaki ya kasance Ubangijin littafin, wanda yake kashewa gami da rayawa, littafi ne wanda ya ƙunshi bayanin soyayya gami da illar butulci da cin amana.
Gabatarwa:
Littafin ‘Rayuwar Bilkisu’, yana da shafuka guda ɗari da sittin da biyar,kuma ya taɓo batutuwa da yawa, wanda suka shafi rayuwa soyayya gami da ƙalubalen da ke cikinta, wanda ya raɗawa littafin suna da ‘Rayuwar Bilkisu’.
Wace ce Bilkisu:
Bilkisu kyakkyawar budurwa ce, mai murmushin narkar da zuciyar Sharfaddeen, saurayin da take fatan ya zama mijinta , kuma uban ‘ya ‘yanta. Amma yau ga shi lokaci ɗaya kawunta yana neman ya kunno mata auren ɗan uwanta Bello babban yaro, kamar yadda mutanen garinsu suke kiran sa. Saboda yadda ya kasance mutum mai son ƙarya da son fantamawa.
Amma ita Bilkisu a rayuwarta, tun asali ma, ba ta ƙaunar auren zumunci, saboda wasu dalilai, wanda marubucin bai faɗa ba.
Bilkisu Mahmud shi ne sunanta, kamar yadda marubucin littafin ya raɗa mata, ta taso cikin tsananin gata da kulawar Baffanta. Ta wanzu cikin wannan gata da kulawa har zuwa lokacin da ta cika shekaru goma sha uku a doron duniya.
Bilkisu ta shiga soyayya da Sharfadden acikin wannan littafin.
Haka rayuwar Bilkisu ta kasance a makaranta, yau da daɗi gobe babu. Ta waje ɗaya take jin daɗi a wannan lokacin, duk Asabar da Lahadi sai ta kirawo Sharfaddeen sun gaisa. Duk sanda suka yi waya sai ta yi masa kuka a kan cewa, duk rintsi, duk wahala, kar ya guje ta. Shi kuwa a ɓangarensa ransa ne yake ɓaci duk sanda ta yi wannan kukan, hanklinsa ya tashi ya rasa me yake masa daɗi. Domin idan akwai abin da ya tsana a dunya to bai wuce ganin kukan ta ba. Abin da Bilkisu ba ta sani ba duk san da take yi masa wannan kukan, shi ma kukan yake yi, saboda yana damuwa da damuwarta
Sharfadden:
A rayuwar Sharfaddeen, ba zai taɓa mantawa da ranar Laraba ba, ranar da ya fara tozali da Bilkisu mai gadon zinare, a garin Kunya a sanadin ziyara da ya kai wa wani abokinsa.
Sharfadden, ya tsunduma cikin son Bilkisu, saboda ita soyayya, aba ce mai wuyar sha’ani gami da ƙalubale, amma ga wani rubutu da na yi akan haka, a littafina mai suna “Tarkon ƙauna”. SO tsuntsu ne, wanda yake kai kawo a tsakanin zukatan mutane mabanbanta, So dausayin farin ciki ne, mai haddasa ƙaruwar farin ciki mara misaltuwa ga masoya, SO ne fitillar da ke haskaka zuciyar wanda suka faɗa cikin kogin soyayya, SO ne tekun da ke gudana a tsakanin zukata mabanbanta, SO shi ne asalin jigon rayuwa, sannan kuma shi ne abin da ke sarrafa ragamar dokin rayuwa bisa hanya managarciya, SO wata bishiya ce wacce take tsirowa a cikin zukatan masoya, SO shi ne sinadarin sadaukantakar zuciya, wanda yake antaya zuciya zuwa cikin kogin madarar tantagaryar ƙauna, SO shi ne maganin da yake iya warkar da mutum daga cutar soyayya matuƙar an dace da abin da ake ƙauna, SO wata guguwa ce wacce take ɗaukar masoyi ko masoyiya zuwa tafkin annurin zinaren hadarin soyayya, idan guguwar SO ta ɗauki mutum sukan iya makancewa akan abin da suke so.
Lokacin da wannan soyayya ta ƙullu, Bilkisu na makaratar kwana a garin Minjibir wato FGC tana
JSS 3.
Jin-jina:
1. Soyayya ita ce jigo acikin al’amuran mutane, shi ma haka marubucin ya nuna mana acikin littafinsa, kamar abin da ya faru akan Alhaji Mahmud zuwa kan Bilkisu da Sharfaddeen
2. Marubucin ya kawo illar zuwa wajen boka. Kamar yadda ya faru da Hajiya Jummai.
3. Littafin ‘Rayuwar Bilkisu’, ya nuna Illar nunawa ɗa gata wacce ta haura ƙa’ida, kamar yadda Hajiya Jummai ta yi wa ɗanta Bello har daga ƙarshe, sai da ya yi sanadiyyar barinta duniya (kashe ta).
4. Littafin ya yi bayani akan mahimmanci addu’a, ko da kuwa mutum yana taimaka wa mutane, saboda duk kirkinka, to wani haushinka yake ji, kuma zai iya ma asiri, kuma ya yi tasiri akanka, kamar yadda sihiri ya yi tasiri akan Alhaji Mahmud.
5. Littafin ya yi nuni akan illar auren dole gami da bin lamurran a hankali.
Kura-kurai:
1. Marubucin ya kawo wani waje, inda jariri yake bayar da labarin yadda aka haife shi, wanda a wannan duniyar ta mu, akwai abin dubawa a ciki. Wato salon rubutun ya ƙwace masa.
2. An samu kuɓucewar salon labarin, acikin rubutunsa.
3. Marubucin ya yi saurin kashe Bilkisu a cikin labarin, wanda ita ce jigon labarinsa.
4. Labarin littafin ya fi ƙarfi a ƙauye, amma bai kawo kalolin abinci da ake ci na Hausawa ba, musamman a ƙauye.
5. Yadda labarin ya nuna, labari ne da ya ƙunshi rayuwar Hausawa a zamanin baya, amma bai yi amfani da sunayen Hausawa ba.
6. Akwai ƙarancin bin ƙa’idojin rubutu, a wasu guraren.