Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce idan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC suka sake lashe zaɓe a 2027, hakan zai lalata makomar ’yan Nijeriya.
El-Rufai, ya faɗi haka ne a Jihar Sakkwato yayin wani gangamin wayar da kan jama’a da jam’iyyar adawa ta ADC, ta shirya.
Ya ce yana goyon bayan wannan haɗaka, kuma zai taimaka wajen ganin ’yan Nijeriya sun sauke APC daga kan mulki.
“Idan muka bar wannan gwamnati ta ci gaba da mulki zuwa karo na biyu, ragowar abin da ya rage na haɗin kai da amincewa tsakanin ‘yan Nijeriya zai lalace.
“ƙasar na iya fuskantar barazana,” in ji shi.
“Wannan dai ta zama gwagwarmaya don ceto rayuwarmu.”
El-Rufai, ya ce dawowarsa siyasa ba don wata riba ko matsayi ba ne, sai don yana ganin gwamnatin yanzu ta gaza.
“Ba don ƙashin kaina nake wannan ba. Na dawo siyasa ne domin na yi wa al’umma hidima. Idan gwamnati ba ta cika alƙawari ba, dole ne na fito na faɗi gaskiya kuma na ɗauki mataki,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa haɗakar ADC an kafa ta ne domin yaƙar manufofin APC.
Ya ce gangamin da aka yi a Sakkwato shi ne farkon matakin neman goyon bayan jama’a a faɗin ƙasar nan.
El-Rufai, wanda ya ɗaya ne daga cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar APC, ya fice daga jam’iyyar a watan Maris, 2025.
Ya koma jam’iyyar SDP, saboda rashin jin daɗin yadda ake tafiyar da mulki a Nijeriya.
