Saki boka, ki kama Allah (2)

Daga SALIHA ABUBAKAR ABDULLAHI ZARIYA

Barkanmu da sake saduwa a shafin iyali na jarida mai farin jini Manhaja. A satin da ya gabata, mun fara shimfiɗa kan wannan darasi na mu, kuma da yardar Allah, za mu ɗora daga inda mu ka tsaya:

Ya ku ‘yan’uwa mata da ba ku ƙaunar kishiya, shin kun san ƙaddarorin da Ubangiji ya rubuto a kanku ko kan ‘ya’yanku mata? Shin ku na da tabbacin cewan ba a ƙaddaro mu su auren mazajen wasu ba, ina batun ƙanwarki, ko yayarki? Gabaɗayansu an faɗa miki su kaɗai za su zauna babu kishiya?

Waɗanda ke ƙin ‘ya’yan kishiya kuma, an faɗa mu ku za ku dawwama ne a cikin duniyar tare da na ku ‘ya’yan? Ba ku tunanin za ku iya mutuwa ku barsu a hannun wasu matan? Ya kuke zaton rayuwarsu za ta kasance in har ba ku riƙe na wasu tsakaninku da Allah ba?

Ina batun waɗanda suka shiga, suka fita wajen ƙasungumin kafirin boka, domin mallake miji, kun manta cewan za ku tsaya gaban Ubangijinku, a yi mu ku hisabi? Me za ku cewa Mahaliccinku ranar gobe ƙiyama?

Ku da kuke neman tarwatsa rayuwar jin daɗin ‘yan’uwanku Musulmai, kun manta duniyar ba matabbata ba ce? Kun manta za ku mutu a turbuɗeku cikin rami, a mayar da ƙasa a rufe, a barku daga ku sai halinku?

Shin kun manta Allah na yafe zunubin bawa tsakaninsa da shi, amma bai taɓa yafe na wanda aka zalunta har sai in ya yafe?

Kun manta akwai hisabi? Me za ku cewa waɗanda kuka ɗauki haƙƙoƙinsu tun daga kan mazajenku har zuwa ‘ya’yanku da iyayenku, domin wasu da dama sun samu ingantacciyar tarbiyya daga gida, ruɗin shaiɗan da duniya kawai suka zaɓa.

To ya za ku yi da haƙƙin addininku da na kanku, saboda tun daga lokacin da kika sa ƙafa kika taka gidan wani boka da sunan biyan buƙata, kike cikin la’anar Allah, balle ki gasgata furucinsa har kuma ki amince, a inda malamai suka nuna ba za a karɓi duk wasu salloli da kika yi ba har kwana arba’in. Wa’iyazubillah!

Ya ku ‘yan’uwa, me yai zafi haka, me mu ke nema cikin wannan duniyar me cike da ƙazanta da ta ke tamkar a sha ruwan tsuntsaye?

A cikin wannan taƙaitacciyar rayuwar da ake mutuwa tamkar ana tafiya da ƙafafu? Yanzun nan za a ga mutum anjima a ce babu shi, ya tafi lahira, ko da ciwo ko babu ciwo.

‘Yan’uwa mu sani, duk shige da ficen da za ku yi bai hana mala’ikar mutuwa ɗaukar rayuwarku idan lokacinku ya yi, wanda ko bokan da kuka ba gaskiya bai isa ya hana miki barin duniyar ba, duk ƙarfin tsafinsa, domin da yana da iko, da bai tafi ba, da yana da iko sa wa, ko hana wa, da bai yi talauci ya zauna a inda yake nan ba cikin ƙazanta da talauci, sai saboda Ubangijinsa da ya dabaibaiyeshi.

Shin a rayuwar irin waɗannan mata me suka tsinta? Waɗanne irin nasorori suka samu dawamamma?

Don haka ‘yan’uwa, ku yi karatun ta natsu, ku yaƙi shaidan, ku dawo bisa hanyar tafarkin gaskiya, ku gaggauta tuba, ko Ubangijin da ya busa mu ku numfashi, ya kuma ba ku damar yin abinda kuka ga dama zai dube ku da idon rahama, ya jiɓinci lamurranku, domin Shi ne mai ikon kowa da komi, Shi ne mai tausayi da jin-ƙan bayinsa, waɗanda idan mu ka kiraye shi zai amsa mana, idan mu ka nemi yayewar tsanani zai yaye mana, idan mu ka roƙe shi zai bayar.

Wanda ke da Allah Gwani, Buwayi gagara misali, me zai sa ku yi sakacin ba shaidan kafa ya ja ku zuwa wuta kuna ji, kuna gani, ya sa ku yawon gidajen mushrikai, kuna kashe dukiyar da mahaliccinku ya ni’imataku da ita cikin jin ƙai da tausayinsa, ku na zubar da ƙima da mutuncinku, domin wasu la’anannun bokayen sai sun aikata zina da ku suke ba ku taimakon da kuka je nema, bayan kuwa ku Musulman ƙwarai ne masu bin sunnar Manzon Tsira Muhammad SAW.

Don haka ‘yan’uwa, ina kira da babbar murya, ku saki boka ku kama Allah, don Shi ne dawamammen Sarki, wanda bai neman komi a wajen kowa, amma kowa na neman komi a wajensa. Wanda Allah ya shiryar haƙƙiƙa ya shiryu. Allah ka ganar da mu, Ka ɗora mu a kan siraɗɗul mustaƙeem.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *