Daga AISHA ASAS
Biyo bayan kammala zaƙulo ɗalibai goma daga ƙaramar Hukumar Sakkwato ta Arewa don ba su damar yin karatu kyauta kamar dai sauran takwarorinta da ke faɗin jihar, shirin Maida Alheri da Alheri ya yi shiri tsaf don cika alƙawarin da ya ɗauka na waiwayar sha’anin yunwa, a ƙoƙarin ganin kowane ɓangare na Jihar Sakkwato ya samu kasonsa a kuɗaɗen da gidauniyar Attahiru Bafarawa ta bayar don rage wa al’ummar jihar raɗaɗin matsin tattalin arziki da a kullum ke ƙara ta’azzara.
A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne shirin na Giving Back Initiative ya ƙaddamar da rabon abinci ga mabuƙata 200 da aka zaƙulo daga gundumomi biyu da ke ƙarshen Sakkwato ta Arewa, wato Sakkwato Garka da kuma Sakkwato Sabon Birni.
Rabon wanda aka gudanar a harabar ofishin Uban Kasa ya samu halartar limaman manyan Masallatan yankin, wato Masallacin Bello da kuma Masallacin Shehu da kuma chiyaman na Sakkwato ta Arewa da ma wasu manyan baƙi da suka sanya albarka da kuma kira ga manyanmu su yi koyi da wannan shiri don ganin sun ceto mutanen su da cikin halin ƙaƙani-kayi.
Tun daga farko wakilan babban kwamiti na gidauniyar Attahiru Bafarawa, sun yi bayanin yadda rabon zai kasance, tare da ƙaddamar da rabon ta hanyar ba da rukuni na farko daga jerin sunayen da za su amfana da wannan tallafin.
Rabon abincin ya watsu ne a tsakanin lungu da saƙo na ƙaramar hukumar, inda aka bada shi ga mabuƙata, uwayen marayu, da kuma masu lalura ta musamman, kuma an ba wa kowanne daga cikinsu rabin buhun gero ko masara da kuma dubu biyar na cefane
Za mu iya cewa, kaso mai yawa sun koma gida cike da farin ciki, tare da godiya ga wannan shirin, da kuma fatan yawaitar mutane irin tsohon gwamnan Jihar Sakkwato kuma Garkuwan Sakkwato.