Sanatoci sun ƙi amincewa da naɗa Ononchie Kwamishinar INEC

Daga AMINA YUSUF ALI

Majalisar Dattawa ta ƙi amincewa da a naɗa Ms Lauretta Onochie a matsayin Kwamishinar Hukumar Zaɓe (INEC) mai wakiltar jihar Delta.

Haka nan Majalisar ta amince da naɗin wasu da aka tura mata sunayensu don tabbatar da su a matsayin kwamishinonin INEC.

Waɗanda Majalisar ta amince da naɗin nasu, su ne; Farfesa Muhammad Sani Kallah (daga Katsina), Farfesa Kunle Ajayi (daga Ekiti), Saidu Ahmad (daga Jigawa), Dr Baba Bila (daga shiyyar Arewa-maso-gabas), sai kuma Farfesa Abdullahi Zuru (daga shiyyar Arewa-maso-yamma).

Naɗin nasu ya biyo bayan amincewa da Majalisar ta yi ne da rahoton da kwamitin tantance waɗanada lamarin ya shafa ya gabatar mata ran Talata.

Majalisar ta yaƙi amincewa da naɗin Onochie ne saboda dalilai masu alaƙa da tsarin yi wa dokar ƙasa ɗa’a.

Da yake gabatar da rahoto ga majalisar, Shugaban Kwamitin, Kabiru Gaya (APC-Kano), ya shaida wa Majalisar cewa ba daidai ba ne a samu mutum biyu daga shiyya guda riƙe matsayin Kwamishinan INEC na ƙasa, wanda a cewarsa hakan ya saɓa wa tsarin doka.

Ya ba da misalin kasancewar Mrs May Agbamuche Mbu daga jihar Delta a matsayin Kwamishinar INEC, tare da cewa Majalisar ta  tsayar da tabbatar da naɗin Farfesa Sani Adam (daga Arewa ta tsakiya) don ci gaba da aikin majalisa.