Anjima Buhari zai gana da sanatoci a fadarsa

Ya zuwa ƙarfe 8 na dare na wannan Talatar ake sa ran Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari zai gana da sanatoci su 109 a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

Sanarwar ganawar na ƙunshe ne cikin wata wasiƙa da Fadar Shugaban Ƙasar ta aika wa sanatocin wanda Shugaban Majalisar, Ahmad Lawan, ya karanta ta yayin zaman majalisar.

A ranar 27 ga Afrilun da ya gabata ne sanatocin suka cim ma matsayar neman ganawa da Buhari domin ba su damar tattauna matsalar tsaron ƙasa da shi.