Sanin Jaji ya jajenta wa waɗanda gobarar Ƙauran-Namoda ta shafa da tallafa musu

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Ƙauran-Namoda/Birnin Magaji, Hon. Aminu Sani Jaji, ya bayyana mutuwar almajirai 17 a iftila’in gobarar Ƙauran-Namoda a matsayin babban rashi ga jiharz Zamfara da ƙasa baki dyaya.

Hon. Jaji a wata sanarwa da ya fitar a Gusau, ya bayyana kaɗuwarsa bisa gobarar, wadda ta lalata Makarantar Malam Ghali da ke ƙaramar hukumar Ƙauran-Namoda a jihar Zamfara, tare da yin sanadin mutuwar daliban 17 tare da jikkata wasu da dama.

Jaji, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Kula da Muhalli na majalisa, ya jajenta wa Shugaban Bola Ahmed Tinubu, Gwamnati da al’ummar Jihar Zamfara, da iyalan yaran da suka rasu sakamakon gobarar.

Ya kuma yi addu’ar Allah Ta’ala ya kiyaye afkuwar irin haka a nan gaba.

Kazalika, wakilinmu ya ruwaito cewa, Jaji ya aika wata tawaga zuwa wajen da lamarin ya faru domin sanin halin da ake ciki, inda kuma ya bayar da tallafin kuɗi da magunguna da kayayyakin agaji ga waɗanda abin ya shafa.

By Babaji