UNDP za ta gina wa ‘yan gudun hijira gidaje 150 a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Hukumar raya ƙasa na majalisar ɗinkin duniya UNDP za ta gina wa ‘yan gudun hijira gidaje guda 150 a garin Jibiya na Jihar Katsina.

Shugaban ƙaramar hukumar Bashir Sabi’u Matan wanda ya sami wakilci na sakataren ƙaramar hukumar Muhammad Lawal Jibiya ya faɗa wa manema labarai haka a garin Jibiya.

Ya ce tuni gwamna Dikko Raɗɗa ya biya Naira miliyan 60 a matsayin diyya ga waɗanda aka amshi filin su domin aikin ginin.

Sakataren ya bayyana cewa wannan koƙari ne da gwamna Dikko Raɗɗa ya yi da haɗin gwiwa da UNDP domin taimakawa yan gudun hijira da hare haren ‘yan bindiga ya shafa.

“Haka kuma gwamnatin jihar Katsina ta tanadi fili da zata gina wa yan gudun hijira wajan koyon sana’o’i”inji Lawal Jibiya.

A cewar sa mafi yawan su yan gudun hijira suna da sana’a kafin su faɗa cikin wannan yanayi.

A ƙoƙarin su na taimakawa jami’an tsaro wajan yaƙi da ta’adanci a yankin, sakataren ya sanar da ce karamar hukumar ke ɗaukan nauyi sayen man fetur da gyaran matar yaki APC domin ƙarfawa su jami’an tsaron .

Ya ce gwamnatin jihar ta ƙaro wasu motocin yaƙi ƙirar APC guda biyu a karamar hukumar.

Malam Dikko Raɗɗa ya ɗauki nauyin haɗin gwiwa na jami’an tsaro da wasu jami’an ƙaramar hukumar zuwa shiga daji na tsawon mako guda domin yaƙar ‘yan ta’adda a dajin jibiya.

By ukarofi