

Daga BELLO A. BABAJI
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya gano cewa Nijeriya tana samun ci-gaba ta fuskar kiwon lafiya ganin yadda marasa lafiya daga Amurka da wasu ƙasashe suke zuwa don a musu dashen ƙoda cikin inganci kuma a farashi mai rahusa.
Ya ce Nijeriya ta zaɓi samar da sauƙin farashi ne a jinya tare da yin sa cikin inganci la’akari da al’ummarta.
Shettima ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyara da Ƙungiyar Likitocin Cutar ƙoda ta Nijeriya (NAN) ta kai masa a Fadar shugaban ƙasa dake Abuja.
Ya bayyana buƙatar zuba hannun-jari a ilimin harkokin likitanci na musamman don ciyar da ɓangaren gaba.
Mataimakin Shugaban ƙasar ya ce a kwanan nan ne aka samu marasa lafiya 13 daga Amurka sun zo Asibitocin Zenith Medical da Kidney Centre a Nijeriya don a musu dashen ƙoda saboda sauƙin farashinsa a ƙasar, ya na mai jingina nasarar hakan da ƙwararrun likitocin da aka samu, waɗanda matakinsu ya ke daidai da na ko’ina a duniya.
Kazalika, Shettima ya ce saboda matsin rayuwa wasu ke sayar da gidajensu ko kuma su dogara da tallafin gwamnatin don a yi musu aikin dashe.
Har’ilayau, ya ce akwai buƙatar Nijeriya ta haɓaka harkar lafiya a kowane mataki don ci-gaban al’umma da kuma janyo ra’ayoyin masu zuba hannun-jari a karatunsa na musamman.
