Majalisar Wakilai za ta ƙirƙiro sabbin jihohi 31

Spread the love

Kudu maso Yamma ya samu kaso mafi yawa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kwamitin Sake Nazarin Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na amajalisar Wakilai ya bayar da shawarar ƙirƙirar ƙarin sababbin jihohi 31 a ƙasar.

Mataimakin kakakin majalisar wakilan aasar, Hon.Benjamin Kalu ne ya bayyana haka lokacin da ya karanto wasiƙar kwamitin, a zaman majalisar da ya jagoranta a ranar Alhamis.

Idan aka amince da buƙatar adadin jihohin Nijeriya zai kai 67.

Ga jerin sabbin jihohin da kwamitin ya bayar da shawarar ƙirƙira daga wasu jihohin ƙasar na yanzu:

Arewa ta Tsakiya – Benue Ala daga jihar Benuwai, Okun daga jihar Kogi, Okura daga jihar Kogi, Confluence daga jihar Kogi, Apa-Agba daga jihar Benuwai, Apa daga jihar Benuwai, Abuja da babban birnin ƙasar. 

Arewa maso Gabas – Amana daga jihar Adamawa, Katagum daga jihar Bauchi, Saɓannah daga jihar Borno, Muri daga jihar Taraba, Arewa maso Yamma, sabuwar Kaduna daga tsohuwar jihar Kaduna, Gurara daga jihar Kaduna, Tiga daga jihar Kano, Kainji daga jihar Kebbi, Ghari daga jihar Kano. 

Kudu maso Gabas – Etiti daga duka jihohin yankin shida, Adada daga jihar Enugu, Urashi daga duka jihohin yankin shida, Orlu daga jihar duka jihohin yankin shida, Aba daga duka jihohin yankin. 

Kudu maso Kudu – Ogoja daga jihar Kuros Ribas, Warri daga jihar Delta, Bori daga jihar Ribas, Obolo daga jihohin Riɓers da Akwa Ibom. 

Kudu maso Yamma – Toru-ebe daga jihohin Delta da Edo da kuma Ondo, Ibadan daga jihar Oyo, Lagoon daga jihar Legas, Ijebu daga jihar Ogun, Oke-Ogun daga jihohin Ogun da Oyo da kuma Osun, Ife-Ijesha daga jihohin Ogun Oyo da kuma Osun.

By ukarofi