Sarauniya Elizabeth, mutuwa ƙarshen dukkan talikai

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Kowace rai lalle wata rana sai ta ɗanɗani ɗacin mutuwa domin mutuwa tamkar gadon dukkan talikai ne. Ba ma sai mutum ya yi wani dogon nazari ba, zai amince cewa dukkan mu za mu mutu yau ne ko gobe ko jibi ko ma shekarar baɗi ko shekaru da dama.

Misalai na da yawa da za mu iya fahimtar haka. Ba wanda ya ke raye a yanzu da wani na sa a yanzu ko a da can bai mutu ba. Ga shi ma ko sakwannin yanar gizo ka zo dubawa zai yi wuya ba ka ga labarin wani ko wata sun mutu ba.

Wani lokacin ma za ka ga jerin labarun mutuwa kusan fiye da biyu. Mutuwa kan zo da sanadin rashin lafiya, hatsarin mota ko na wani abu daban, gamuwa da ajali ko ba ciwo da dai sauran su. Hakanan in Allah ya ba wa mutum damar ziyartar maƙabarta zai ƙara tabbatar da cewa mutane na mutuwa.

Ka gwada ziyartar maƙabarta wannan makon, ka ɗage ƙafa zuwa mako mai zuwa, haƙiƙa in ka dawo za ka ga ƙarin jerin layi ko sabbin layukan kaburbura. Duk mai hankali zai ɗauki hakan a matsayin tunatarwa cewa shi ma ya na tafe kan wannan hanya da ba a batan kai.

Kazalika ya zama wa’azi na ƙoƙarin amfani da damar rayuwa wajen aikata auyukan kwarai don girbar riba in an koma ga mahalicci. Rai kyauta ne daga mai Mallakar Sammai da Ƙassai don haka dabarar likita ba ta dauwamar da mutum a raye ko in ya mutu a a ma sa allurar sabon rai don cigaba da rayuwa a doron ƙasa.

Ba tantama in da ana samun rain a sayarwa da wasu sun saye rayukan da duk za a kera su tanada don amfanin kan su da iyalansu. Manyan shugabannin duniya sun mutu, manyan barade sun mutu, manyan sarakuna sun mutu, manyan masu kuɗi sun mutu, manyan masu ilimi sun mutu; kuma mutuwar duk ɗaya ce ba wanda zai zulle ma ta kuma babu rai na sayarwa bayan an mutu.

Ita wannan mutuwa da kan ɗauke manyan jagorori da masu hannu da shuni, ita ce dai kan ɗauke talakan talak da ko a na sayar da rai ba shi da kuɗin saya. Babban abin la’akari shi ne mutum ba za ta bar kowa ba sai ikon Allah. Idan talaka ya mutu saboda tunanin bai samu ƙwarerren likita ko ingantaccen magani ya sha ba, ai duk kula da mai hannu da shuni da ganin ƙwararrun likitoci ba ya hana in ajalin ya zo a tafi.

Ina dabarar ɗan adam in a na maganar mutuwa? Ina jami’an tsaro masu riƙe manyan bindiga don tsaron ran wani maigidansu, yayin da mutuwa ta zo ɗaukar ransa? In har ɗan adam ba shi da iko kan mutuwa to ya dace ya dau rayuwa cikin sauƙi da shuka alheri dare da rana har kafin ranar tafiya ta zo.

Da zarar Imani da cewa lalle akwai mutuwa da ba makawa ya yi ƙarfi a zuciyar mutum za ka ga wani lokacin ya na zubar da hawaye da kankan da kai don sanin cewa shi ba mai dauwama ba ne kuma duk daɗi zai ƙare duk daren daɗewa.

A makon jiya ne labari ya bayyana na mutuwar sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu wacce in ka deve Sarki Louis na Faransa da ya mutu a 1715 ya na mai shekaru 72 a gadon sarautar ƙasa mai ’yanci, sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu ce ta fi kowa ne mai sarauta daɗewa a karagar mulkin babbar ƙasa mai ’yanci ta na mai shekaru 70 a kan gado.

Mahaifiyar ta Elizabeth matar Sarki George ta share shekaru 101 a duniya kafin ta mutu a shekara ta 2002. Wannan ya nuna bayan mutuwar mijin ta Sarki George a 1952, ta qara shekaru 50 a duniya sannan ta mutu. A nan za mu lura sarauniyar da mahaifiyar ta, sun samu nisan kwana a duniya kafin mutuwa.

Darasi a nan shi ne ita mutuwa na jiran kowa duk tsawon kwana wataran za ta zo ta ɗauka kuma duk gata ko rashin gatan mutum. Dan ta Yarima Charles wanda yanzu ya gaji sarauta ya share shekaru 50 ya na matsayin Yarima mai jiran gado kafin samun sarauta ya na mai shekaru 73 a duniya.

Tarihi ya nuna Charles ne mafi daɗewa a tarihin ƙasarsa a matsayin mai jiran gado kuma shi ne mafi yawan shekaru a lokacin hawa sarauta. Mahaifiyarsa Elizabeth ta hau sarauta ta na matashiya mai shekaru 26. Idan taliki ya mutu juyayi ba ya iya tayar da shi, yawan ta’aziyya ba ya iya tayar da shi, kabari na alfarma ba ya iya tayar da shi.

Abu mafi ma’ana a faɗa a nan shi ne in mutum ya mutu ayyukansa na alheri za su riƙa sa a na tunawa da shi hakanan in ya haifi ’ya’ya ya kuma yi mu su tarbiyya mai kyau za su sa a riƙa tunawa da shi. Ya kamata a riqa addu’ar fatar bayan mutuwa a riƙa tunawa da alherin mutum ya zama ya rinjayi akasin sa da ya aikata.

A sarauta mutuwa ce a ka fi sani ta na sa a samu sabon sarki kuma tun mai sarauta ya na raye ya kan so ya naɗa magajinsa. A manyan masarautu irin na Birtaniya, a kan naɗa magaji ga sarki don an san tabbas wataran sarkin zai mutu. Hasalima sarkin ko sarauniyar kan naɗa wanda zai yi gado bayan mutuwarsu.

Tuni Sarki Charles ya naɗa ɗan sa Yarima William ya zama mai jiran gado. Kun ga duk dadin sarauta ba ta hana shiryawa mutuwa don karɓar ragama da magaji zai yi. Duk da ba a san gawar fari ba, amma koyaushe manyan sarakuna na da masu jiran sarauta da zarar sun kau sai a naɗa magada kawai.

Irin wannan tsarin kan sa ba a ɓata wani loakci wajen naɗa magaji don dama ya na nan ya na jira kuma zai fara aiki nan ta ke ya kuma jagoranci jana’izar wanda ya riga mu gidan gaskiya.

Ƙasashen Afirika da dama za su yi matuƙar juyayin mutuwar Sarauniya Elizabeth II – Sa’idu Ahmed Dukawa:

Masanin Kimiyyar Siyasar Duniya na Jami’ar Bayero ta Kano Dakta Sa’idu Ahmed Dukawa ya ce, ƙasashen Afirka da dama za su yi juyayin mutuwar sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu don rawar da ta taka wajen karɓar ’yancinsu.

Elizabeth ta hau sarauta a daidai lokacin da ake dosar neman ’yancin kai ga ƙasashen da Birtnaiya ta yi wa mulkin mallaka. Matsayin na ta ya ba ta damar ganawa da ’yan gwagwarmayar ƙasashe masu shekarun da ke nesa da na ta a loakcin. Kuma kasancewar ta saruniyar babbar daula, ya zama wajibi a girmama ta da neman amincewar ta kan lamuran ’yanci. Tattalin arziki da tsarin mulkin ƙasashen da a ka yi wa mulkin mallaka.

Dakta Dukawa ya ƙara da cewa, yawancin mutane sun tashi da jin sunan sarauniyar wacce ta zo da kan ta ziyarar aiki ƙasashen kuma ta ƙulla hulɗa mai ƙarfi da manyan jagororin ƙasashen waɗanda akasarinsu, sun daze da barin duniya ‘duk mai shekara 40 zuwa 50 har 70 ya tashi ya na jin sunan sarauniya Elizabeth, don haka yau an wayi gari mai irin wannan matsayi ta kau daga duniya’.

Dukawa na ganin samun cike gurbin da marigayiyar ta bari na da wuya don yadda ta daɗe da samun gogewa a tsawon shekaru, sai dai a na fata Yarima Charles da zai zama sabon sarki ya samu gogewa ko tarbiyantuwa daga mahaifiyar tasa.

Marigayiya Elizabeth ta yi mu’amalar kirki da iyayen Nijeriya irin marigayi firaminista Abubakar Tafawa Ɓalewa da firimiya Ahmadu Bello Sardauna har da ba su lambar girma ta masarautar Ingila da a ka ambatawa ko rubutawa gabanin sunan su wato SA ko kuma SIR a turance.

Marigayiya Sarauniya Elizabeth mace ce da ta fi wasu mazan taka rawa a siyasar duniya – Dakta Idi Hong:

Tsohon Ministan Harkokin Wajen Nijeriya Dakta Aliyu Idi Hong ya zayyana marigayiya sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu a matsayin wacce ta yi wa shugabnni maza da dama zarra a sha’anin gogewa wajen siyasar duniya.

Dakta Hong wanda ya ke sharhi kan mutuwar sarauniyar da hawan karagar sabon sarki Charles, ya ce, rashin tsoma bakinta a lamuran gwamnatin siyasa da takaita kan ta kan mulkin ta na gargajiya, ya ba wa Elizabeth martaba ‘gaskiya mace ce Allah ya halicce ta a mace amma a nuna shugabanci da kuma nuna kara da yadda a ke shugabanci, ai ta yi abubuwa da dama da mazaje ba su iya irin su ba’.

Tsohon ministan ya ƙara da cewa kusan in an duba alƙaluman mutanen duniya na yanzu kusan kashi 70% sun rayu a zamanin da Elizabeth ta yi sarauta daga hawan ta karaga a 1952.

Dakta Hong ya haƙƙaƙe cewa in ka deɓe wasu rigingimu da su ka shafi ’ya’yan ta, za a yi wa marigayiya Elizabeth shaida da rayuwa mai cike da dattaku da kamun kai.

Kammalawa;

Shawara biyar mai muhimmanci ga talikai kamar haka: ka tanadi tsufan ka tun ka na da ƙuruciya, ka tanadi rashin lafiyarka, tun ka na da lafiya, ka tanadi lokacin ka tun kafin shagaltuwa da dawainiya, ka tanadi arzikin ka tun kafin yiwuwar karayarsa ta zo ma ka, ka tanadi mutuwar ka tun ka na da rai. Allah ya sa mu gama da duniya lafiya.