Gwamnati ce babbar matsalar Nijeriya (2)

Manhaja logo

A cigaba da rubutu da na ɗauko game da matsaloli da muke ta fuskanta a ƙasar nan, na yi bayani yadda gwamnatin ta ke nuna gazawa harkokin tattalin arziki da kuma fannin ilimi. A makon jiya, na tsaya ne akan cewa zamu yi bayani akan taɓarɓarewar rashin tsaro.

Harjar tsaro, wani yanayi ne da ke ɓata tattalin arzikin ƙasa. Wanda ba iya nan ba, zamu iya cewa tuk abinda babu kwanciyar hankali ciki to babu cigaba. Kuɗi na tafi saboda harkar tsaro, kuma dukiya na salwanta ga uwa uba kuma rashin muhalli da kuma walwala da al’umma ke ciki.

Haƙiƙa nan ma zamu iya cewa gwamnatin Nijeriya na iya ƙoƙarin ta wajen daƙile matsalar, amman nan ma an gudu ba tsira ba, domin salo da gwamnatin ke ɗauka ba zai taba kawo ƙarshen lamarin ba har abadan.

Kafin mu ci gaba, bari mu ɗan bada misali. Mai karatu kayi shiru, kaɗan natsu sannan ka yi tunani tare da nazari, kaine nan, kana da gida da iyalai 20, sai wani faɗa ya taso tsakanin matan ka da wasu ’ya’yan matan.

Akwai makocin ka, shi din makeri ne, kai baka iya kyera komai ba, amman kasan makocin ka na kyera adduna da wuka. Bayan rigima ta kaure a gidan ka sai aka samu wani ɗan ka ya sari ɗayan ɗan ka da adda, sai jini ya zuba, baka tsaya bincike me ya haɗa su ba, me dalilin faruwan hakan ba, kawai sai kaima kaje sayan adda a wajen makocin ka don yaƙar ɗanka da ya sari ɗanka.

Kuɗin ka ya fita, kuɗin ɗan ka ya fita. Misali ɗan ka ya fitar da 1,000 ɗan sayan makami don ya kashe dayan ɗan ka, kai kuma ka saya makami na 1,500 dan yaqar ɗayan ɗanka. Wataƙila a gidan ka kuna da 5,000 ne kacal, kai ka cire 1,500, shi kuma ɗanka ya cire 1,000, kaga 2,500 ya fita daga tattalin arzikin gidanka don magance matsalar da ta faru.

Duk wannan abin da ya faru, baka tsaya kayi tunanin me sanadin faruwan wannan abin ba, kuma a ina ɗan ka ya sayo makamin da har ya illata ɗaya ɗanka ba. Ka cire kuɗi ɗanka ma haka, sai ya zamana kuna yaƙan junan ku shi kuma makocin ka arzikin shi na karuwa, saboda yaƙi da ya ke faruwa a cikin gidan ka.

Dan Allah kayi tunani, shin makocin ka zai zo yakin nan ya kare? Shin ka ɗauko hanyar kawo ƙarshen rikicin cikin gidan ka kuwa?

To’ abinda yake faruwa a Nijeriya kenan. Muna sayan makami a waje don yaƙar ’yan ta’adda na cikin gida. Su ma ’yan ta’addan na sayen makamai daga waje don yaƙar gwamnatin gidan su. Duk duka kuɗin ƙasar ne ke fita. Me yasa gwamnatin ba zata dau mataki ba?

Idan aka kama ’yan ta’adda, ayi bincike, wannan makamai da ake kamewa tare da za su, a ina aka samu? Wace kasa ce ta kyera ta? Ai akwai jakadanci tsakanin ko wacce kasa da Nijeriya. Sai a tuntuve su, tayaya suka sayar wa ’yan ta’addan Nijeriya kayan yaƙi? Idan suka ki ɗaukar mataki, Nijeriya sai ta ɗauka, zata iya yin barazanar yanke alaƙa tsakanin ta da ƙasar da ke sayar wa ’yan ta’adda makamai, kaga ko wace ƙasa ce dole ta ji tsoro. Amman Nijeriya ina. Ba ruwan ta. Kullum kuɗi na fita don sayen makamai. Maimakon yaƙin ya ƙare, sai faɗa ƙaruwa ya ke yi.

A shekarun baya, yaƙin Boko Haram iya Jihar Borno da Yobe da Adamawa ne kawai, sauran jihohin suna zaman lafiya. Kamar Zamfara da Sokoto da Neja, duk ba zaka taɓa jin labarin ’yan bindiga ba, amman yanzu fa?

Gwamnati ta ce, ta rufe bodoji don samar da tsaro, yanzu ina tsaron ta ke? Hasali ma an fi zaman lafiya kafin yunƙurin rufe boda.

Jami’an tsaro sam sam basu da horo. Ma’ana ba a hora su hanyar da za su kawo ƙarshen ta’addanci ba, hasalima waɗanda ba su ji ba ba su gani ba su ke mutuwa, su ke rasa dukiya, su ke rasa muhalli, su ke rasa rayuka. Basu hannu a lamarin sun fi kowa zaman lafiya.

Janarori na yanzu, ba su san kan aiki ba. Janar na zama a ofis cikin masuburbuɗar sanyi amman yana tsara yadda za a yi a yaƙi ɗan ta’adda. A wajen shi duk wanda baya shan AC ɗan ta’adda ne. Shi yasa zaka ga da zarar sojoji sun fara aiki, mafi yawan mutane da suke mutuwa talakawa ne, waɗanada ba ruwan su. Sai abin ya yi yawa sai kaji su ce ai kuskure ne.

A cikin mutanen da suka mutu a Nijeriya saboda wannan rikicin, sojoji sun kashe 40%, ’yan ta’adda kuma 60%. Mu haɗu a mako mai zuwa don cigaba. Allah ya tausaya mana, Ameen.

Daga Mohammed Albarno. O8034400338,
[email protected].