Nijeriya da ƙasar Poland za su sabunta alaƙar kasuwanci tsakaninsu

Daga AMINA YUSUF ALI

Shugaban ƙasar Nijeriya, Janar Muhammadu Buhari mai ritaya ya bayyana cewa, akwai buƙatar a ƙara ɗabbaƙa alaƙar cinikayya dake tsakanin ƙasar Poland da Nijeriya. Domin a cewar sa, duk da dai da ma alaƙarsa tana nan tsahon shekaru 60 da ƙulluwa, akwai buqatar ƙara ƙarfafa ta saboda sanyi da ya ce yana ganin ta yi.

“Za mu so mu ga an samu haɓakar kasuwanci tsakanin ƙasashen guda biyu, domin a halin yanzu hulɗar kasuwanci ta yi ƙasa sosai tsakanin ƙasashen biyu duk da tsahon lokacin da aka ɗauka ana hada-hada tsakanin ƙasashen guda biyu”.

Buhari ne ya bayyana haka a taron ganawar sirri da suka yi da shi da takwaransa, Andrzej Duda, na ƙasar Poland ranar Talatar da ta gabata a fadar shugaban ƙasa dake Birnin Tarayyar Abuja.

A yayin taron, shugabannin ƙasashen biyu sun rattaba hannu a kan takardar fahimtar juna a kan hada-hadar kasuwancin amfanin gona a tsakanin ƙasashensu.

Waɗannan al’amuran sun faru ne yayin da Shugaba Duda na ƙasar Poland ya kawo ziyarar ƙasa ta kwana biyu zuwa Nijeriya.

Hakazalika, shugaban ƙasar Poland ɗin ya shirya tattaunawa tare da kafar yaɗa labarai ta BBC bayan sun kammala taron na ranar Alhamis.

A taron ganawar dai Buhari ya yaba wa shugaban a kan irin gudunmowar da ya bayar wajen rungumar yan gudun hijira da yaƙin Yukiren da Rasha ya rutsa da su suka gudu Poland. Cikinsu a cewar sa, wanda akwai ‘yan Nijeriya masu yawan gaske.

Sannan kuma ya ce Nijeriya ba za ta tava mantawa da irin hoɓɓasar da ƙasar Poland ta ba wa Nijeriya a ɓangaren ilimi da tsaro.

Don haka a cewar sa, ƙulla alaƙar kasuwancin da ƙasashen guda biyu za su yi abu ne da zai sa dukkan ƙasashen guda biyu su rabauta. Kamar da yadda a cewar sa suka rabauta da haɗin gwiwar ƙasashen a fannin ilimi.

Wannan dai shi ne karo na farko da shugaban ƙasar Poland ya fara ziyarar Nijeriya tun shekaru 60 da suka wuce.