2023: Tikitin Musulmi da Musulmi tsantsar yaudara ce, inji Sheikh Gumi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana tikitin tsayawa takarar Musulmi da Musulmi ko Musulmi da Musulma a matsayin yaudara, yana mai cewa abin da ƙasa ke buƙata a 2023 gogaggen shugaba ne da zai iya haɗa kan al’umma. Kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Ya ce Nijeriya ba ta buqatar ƙaramin ɗan siyasa a matsayin shugaban ƙasa, sai dai gogaggen ɗan siyasa da zai jagoranci ta a zaɓen 2023 mai zuwa.
Ya kuma shawarci ‘yan Nijeriya su kawar da siyasar ƙabilanci a wannan karni na 21, kuma su haɗa kai a matsayin al’umma ɗaya dunƙulalliya domin ci gaban ƙasa.

Da yake magana a wata hira da aka yi da shi kan babban zave mai zuwa da kuma halin da al’ummar ƙasar nan ke ciki, Gumi ya ce babu laifi ‘yan siyasa sun yi takara sau da yawa, suna neman nasara.

Da yake jawabin kan Atiku Abubakar Gumi ya ce: “Nijeriya na buqatar gogaggen ɗan siyasa. Ba ma buƙatar ƙaramin ɗan siyasa ya zama Shugaban Ƙasa. Halin da ake ciki a Nijeriya a yau yana buƙatar gogaggen ɗan siyasa don warware shi,” inji shi.

A gefe guda da yake tsokaci kan kan Tinubu wanda ya ce lokacin sa ne ya zama Shugaban Ƙasa, Sheikh Gumi ya ce, “bai dace ba ya ce lokacin sa ne. Babu dalilin da zai ce lokacina ne. Kar ku ce lokaci na ne domin idan mutane kamarku za su zaɓe ku. Shi ma’aikaci ne nagari, zai iya yi. Tikitin Musulmi da Musulmi ba wajibi ba ne ba.

“Dukkanmu mun sani, duk waɗannan ‘yan siyasa suna neman ƙuri’u ne. Tikitin Musulmi da Musulmi shi ne, bari in yi amfani da harshen Hausa, wayo (yaudara). Ba addini ba ne. Ko zai yi aiki ko a’a, ba na son yin yaudara, amma akwai matsaloli da yawa. Hasali ma, dukkan jam’iyyun siyasa suna da nasu matsalolin. Tikitin Musulmi da Musulmi zai zama gwajin dakin gwaje-gwaje don wasu su yi koyi a nan gaba ko a’a.”

Akan Peter Obi ya ce, “matasan da ke biye da shi sun rabu kamar manya. Yana buƙatar ya kai ga sauran sassan ’yan Nijeriya. Dogaro ga matasa kaɗai ba zai wadatar da shi ba. Dole ne ya kasance a ko’ina, kuma kada ya bar siyasar zuwa yanki ɗaya kaɗai.”

Sheikh Gumi ya yi gargaɗin cewa idan aka zaɓi ɗan siyasa maras gogewa a kan karagar mulki, zai yi wahala a iya yi wa al’umma aiki yadda ya kamata.

Sheikh Gumi ya bayyana cewa ya ɗauki tsawon watanni shida, kafin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa ministoci da jami’an gwamnati saboda shi (Buhari) ɗan siyasa ne maras gogewa.

A ƙarshe ya cigaba da cewa, rashin adalci da talauci ne ke haddasa rashin tsaro a ƙasar nan, inda ya ƙara da cewa shekaru bakwai na mulkin Shugaba Buhari kusan kowane ɗan Nijeriya yana jin raɗaɗin quncin rayuwa da matsin tattalin arzikin da ƙasar nan ke fuskata.