Shugaban Hukumar Kula Da ‘Yan Sanda, Muslihu Smith, ya yi murabus

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Hukumar Kula da ‘Yan Sandan Nijeriya (PSC), Musilihu Smith ya yi murabus daga kan muƙaminsa.

Wannan matakin dai na zuwa ne bayan rashin jituwa da kai ruwa rana da aka yi ta samu a tsakanin hukumar da Sufeto Janar na ‘yan sandan Nijeriya, Usman Baba Alkali, dangane da batun ɗaukar sabbin ‘yan sanda, ƙarin girma wa jami’ai, ɗaukar kwansitabul da wasu jami’ai.

Lamarin har ta kai Majalisar Ƙoli na hukumar ta buƙaci Smith da ya yi murabus cikin ruwan sanyi kuma ya amince da yin haka.

Smith, wanda tsohon Sufeto Janar na ‘yan sanda ne, ana sa ran zai miqa ragamar mulkin hukumar ga Justice Clara Ogunbiyi (mai ritaya) wanda shi ne wakilin sashin shari’a a hukumar.

Kakakin hukumar kula da harkokin ‘yan sandan Nijeriya, Ikechukwu Ani, ya tabbatar da ajiye aikin Mista Musilihu Smith a ranar Laraba.

Manhaja Hausa ta naƙalto cewa an ɗauki ‘yan kwanaki ana kai ruwa rana a tsakanin ɓangarorin biyu wanda a dokance hukumar ce ke da damar gudanar da aikin ɗaukar ‘yan sanda.

Ita dai PSC ta wallafa tallar ɗaukan sabbin jami’an ‘yan sanda masu muƙamin kwansitabul (constables) tare da buƙatar masu sha’awar nema da su cika buƙatar hakan a shafinta.

Sai dai kuma daga baya rundunar ‘yan sanda ta nemi jama’a da su yi watsi da wannan sanarwar, ta qage kai da fata cewa shirye-shiryen ɗaukar ikonta ne.

Bisa wannan rashin jituwa da fahimtar juna da aka samu, a ranar 24 g watan Agustan, haɗakar ƙungiyar hukumar kula da ‘yan sanda suka ayyana tafiya yajin aikin sai baba ta gani ga hukumar gudanarwa dangane da abin da suka kira saɓa yarjejeniya.

A wata hira da Muryar Amurka ta yi da Hajiya Naja’atu Mohammed, kwamishiniya a hukumar ‘yan sandan, ta tabbatar da murabus ɗin shugaban nasu.

“Da ma ka san ofis ɗin a rufe yake, ana ta zanga-zangar cewa abubuwan da yake yi ba ya kyautawa.

A cewar Hajiya Naja’atu, “an shirya za a yi taro tare da shugaban hukumar da safe amma sai bai bayyana ba, tana mai cewa hakan ya sa aka ɗage zaman zuwa ƙarfe biyu.

“Da muka zo ƙarfe biyu sai muka ga takardar cewa ya yi murabus, ya je ya kai wa shugaban ƙasa, kuma shugaban ƙasa ya ce an karvi murabus ɗin na sa,” inji Hajiya Naja’atu.