Taron MƊD: Yau Buhari zai tafi Amurka

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Yau Lahadi ake sa ran Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari zai bar Nijeriya zuwa ƙasar Amurka don halartar taron Malajisar Ɗinkin Duniya karo na 77 (UNGA77).

Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Femi Adesina ya fitar.

A cewar Adesina, Buhari zai bayyana bayanan ƙasa ga taron Majalisar a ranar Laraba, 21 ga Satumba, 2022.

Kazalika, ana sa ran Buhari ya gudanar da wasu ayyuka tsakani da wasu hukumomi yayin ziyarar kana kafin ya komo Nijeriya ranar Litinin, 26 ga Satumba, 26, 2022.

Sanarwar ta ce, “A ranar Lahadi, 18 ga Satumba Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari zai bar Abuja zuwa Amurka don halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 77 (UNGA77).”

Haka nan, sanarwar ta ce taron zai maida hankali ne wajen tattauna wasu ƙalubalen da duniya ke fuskanta, ciki har da batun yaƙin Ukraine da na makamashin gas da dumamar yanayi da annobar Korona da sauransu.

By Editor