Kusantowar yaƙin neman zaɓen 2023

Nan da kwanaki kaɗan za a fara gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a hukumance. Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), wacce ke da hurumin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓe, ta sanya ranar 28 ga watan Satumba domin fara gudanar da ayyukan.

Zaven 2023 na da matuƙar muhimmanci ga ɗorewar dimokaraɗiyyarmu da ƙasa baki ɗaya. Tuni dai yanayin siyasa ya tashi yayin da ‘yan takarar shugaban ƙasa ke yin alƙawura da yawa. Ƙasar na cikin tsaka mai wuya saboda ɗimbin ƙalubalen da ta ke ci gaba da fuskanta.

Saboda ƙaruwar rashin tsaro, talauci da rashin aikin yi, an shiga wani irin yanayi a ƙasar. Duk waɗannan abubuwan suna faruwa ne musamman saboda yadda muka yi rashin sa’a na rashin shugabanci nagari a kowane mataki na mulki.

Yayin da jam’iyyun siyasa ke shirin fara yaƙin neman zace a ƙarshen wannan wata, wasu daga cikin waɗannan batutuwa za su kunno kai. Don haka ya zama wajibi a ja hankalin ’yan takara da jam’iyyunsu da magoya bayansu kan buƙatar yin yaƙin neman zaɓe da ya shafi muhimman batutuwa.

Lokaci na ƙabilanci ko addini, nuna wariya ko addini da maganganun ƙiyayya ya ƙare. Ko kaɗan bai kamata wani ɗan takara ko magoya bayansa su yi amfani da irin waɗannan kalamai masu tayar da hankali a yaƙin neman zave mai zuwa ba.

Talauci, yunwa, rashin tsaro, rashin aikin yi da sauran su ba su da launin ƙabilanci ko addini. Abin da ya shafi al’ummar Arewa shi ma ya shafi mutanen Kudu, walau Kiristoci, Musulmi ko masu bin addinin gargajiya.

Kusan kowane sashe yana buqatar gyarawa. Tattalin arzikin ƙasa ya faɗi ƙasa warwas. Yawan rashin aikin yi ya haura kashi 30 cikin ɗari. Adadin hauhawar farashin kayayyaki a halin yanzu ya kai kusan kashi 19.64 cikin ɗari. Miliyoyin ’yan Nijeriya ne ke fama da yunwa yayin da ’yan ƙasar kusan miliyan 100 suka maƙale a cikin ramin talauci.

Muna da tarihin da ba za a iya mantawa da shi ba a matsayin babban birnin talauci na duniya. Farashin canjin dala a kasuwar bayan fage ya kai kusan Naira 700 a dala ɗaya. Bashin ƙasar nan ya kai Naira tiriliyan 41.6, kuma dul da haka ana yin lissafin zai ƙara ƙaruwa nan da shekara mai zuwa.

A ma’aunin hankali, gaskiya babu wani cigaban da aka samu. ‘Yan fashin daji da ‘yan ta’adda suna ta’addancin ‘yan ƙasa. Ana satar matafiya yadda ake so kuma ana yin garkuwa da su don neman fansa. Ana kashe waɗanda kwanansu ya ƙare.

Makarantu da wuraren ibada ba su tsira ba. Dubban ɗalibai ne suka mutu. A watan Yunin da ya gabata ne wasu ’yan ta’adda suka kai farmaki cocin St. Francis Catholic Church, Owo, a Jihar Ondo inda suka kashe mutane aƙalla 40. Jerin hare-haren makamancin wannan na zama ruwan dare.

Ɓangaren ilimi da kiwon lafiya ma suna baya. Babu wani abu da ya nuna halin rashin kyawun tsarin iliminmu kamar yajin aikin da ƙungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ke yi a halin yanzu.

Ƙungiyar ta tsunduma yajin aikin mai cike da ruɗani tun a watan Fabrairun 2022 kuma babu alamar zai kawo ƙarshe a nan kusa. Wannan ya gurgunta harkokin ilimi da sauran ayyukan a jami’o’in gwamnati. Har ila yau, fannin kiwon lafiya ya koma yajin aiki.

Ƙungiyar Likitoci ta ƙasa (NARD) ta samu dalilin shiga yajin aiki a lokuta da dama kan batutuwan da suka shafi walwala. Sakamakon rashin gamsuwa da aikin yi a ƙasar, dubban likitocinmu sun yi hijira zuwa ƙasashen ƙetare don neman mafaka.

An ba da rahoton cewa, adadin likitocin da Nijeriya ta horar da su da suka yi hijira zuwa Birtaniya kaɗai ya kai 10,096 a ranar 30 ga Agusta, 2022. Kimanin 6.068 daga cikin wannan adadin sun koma Birtaniya tun lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya fara mulkin ƙasar a shekarar 2015.

Ya kamata ‘yan takarar shugaban qasa su gaya wa ‘yan Najeriya yadda suke da niyyar ceto ƙasar daga waɗannan matsaloli. Kamata ya yi su bayyana yadda za su gyara tattalin arziki da warware ƙalubalen da suka shafi tsaro, samar da ababen more rayuwa, ilimi, sufuri, lafiya, wasanni da sauran fannoni a cikin ƙayyadaddun lokaci.

Mun yarda cewa babu wanda ke da dukkan amsoshin matsalolin ƙasar, amma dole ne su sami amsoshin wasu batutuwan da ke damun ‘yan Nijeriya a yau.

Don cimma wannan, muna buƙatar samun samfuri wanda zai fitar da yaƙin. Yakamata Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta samar da irin wannan samfuri tare da wayar da kan ’yan Nijeriya muhimmancin zaɓen domin mutane su san abin da suke ciki.

Hukumar zaven ta fara ta hanyar hana kamfen a coci-coci da masallatai. Ana buƙatar ƙarin irin waɗannan abubuwan. Alal misali, bai kamata a sami ’yan daba ko tashin hankali a lokacin yaqin neman zaɓe ba. Magoya bayan jam’iyyun siyasa dole ne su gudanar da kansu cikin lumana.

A bar yaƙin neman zave ya zamanto bisa tsari, kuma ba don komai ba wata gwamnatin jiha ta hana ’yan jam’iyyar adawa yin kamfen ko kafa allunan talla a jihohinsu kamar yadda aka ruwaito a wasu sassan. Dole ne a hukunta duk wanda keta waɗannan ƙa’idojin. Dole ne yaƙin neman zaɓe ya kasance cikin lumana.

Kyakkyawan jagoranci da shugabanci nagari na iya tabbatar da walwala da jin daɗin ’yan ƙasa. Mutane suna tsammanin cewa duk wanda suka zava dole ne ya sami damar magance matsalolin da al’ummar ƙasar ke fuskanta.

Duk da kasancewarsa baƙar fata, an zavi tsohon shugaban Ƙasar Amurka Barack Obama (Amurka) kan muƙaminsa saboda bajinta da haziƙan tunaninsa. Nijeriya na buƙatar irin wannan shugabanci a yau. Dole ne mu daidaita a 2023 idan har yanzu muna son samun ƙasa mai suna Nijeriya.