Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta cafke sojan bogi

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau

Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta kama wani sojan bogi mai suna Zainu Lawal da ke bayyana kansa a matsayin jami’in sojan Nijeriya.

Kakakin rundunar, Sp. Muhammad Shehu ne ya bayyana haka a wata ganawa da manema labarai lokacin da yake gabatar da wanda ake zargin tare da wasu ‘yan ta’adda a hedikwatar rundunar da ke Gusau ya bayyana hakan yau Asabar.

Sp. Shehu ya bayana cewar kayayyakin laifin da aka gano daga gare shi sun haɗa da, bindigu ƙirar revolver, 4 Cartridge, I D Card din soja na bogi da kuma kakin soja ɗaya.

“A ranar 14 ga Satumba, 2022, Jami’an ‘Yan Sanda ƙwararru daga hedkwatar ‘yan sandan mu sun yi aiki da bayanan sirri game da wasu ayyukan da ake zargin wanda ake zargi da aikatawa.

“Wanda ake zargin wanda ya yi iƙirarin cewa shi tsohon soja ne, an kama shi ne ɗauke da wata bindiga ƙirar revolver a gida, kakin soja, katin shaidar soja na bogi da sauran muggan makamai,” inji shi.

Sp. Shehu ya ci gaba da cewa, rundunar ‘yan sandan na gudanar da bincike mai zurfi domin bankaɗo al’amuran da suka shafi mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba da wanda ake zargin.

A halin da ake ciki rundunar ta kama wasu mutane shida waɗanda suka ƙware wajen bai wa ‘yan ta’adda bayanai da Kuma Samar masu makamai da alburusai.

Waɗanda ake zargin dai sun haɗa da Jamilu Kawali aka Tailor da Lawal Ibrahim Galadima na karamar hukumar Ƙaura Namoda da Surajo Idris mai unguwar Tudun wada Gusau da Amadu Rufa’i na ƙaramar hukumar Birnin Magaji da Alhasan Lawali da Mansur Usman dukkansu daga ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar.

“A ranar 12 ga Satumba, 2022, waɗanda ake zargin da aka lissafa a sama, ‘yan ƙungiyar asiri ne da ke haɗa kai da ‘yan bindiga domin ta’addancin mutanen Gusau, K/Namoda, Tsafe, Bungudu LGAs da kewaye.

“Ayyukan wannan ƙungiyar ta haɗin gwiwa shine bayar da bayanai ga ‘yan bindiga domin sauƙaƙa musu kai hare-hare a cikin al’umma tare da yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

“kazalika, wani ɓangare ne na ayyukansu na karɓar miliyoyin Naira don samo makamai da kakin soji ga ‘yan bindiga,” a cewar Sp. Shehu.