Ɗaliban Ghana 140 ne suka samu guraben ƙaro karatu na Jakadan Ƙasar Sin

daga CMG HAUSA

Ɗaliban ƙasar Ghana 140 ne suka samu guraben ƙaro karatu na jakadan ƙasar Sin dake ƙasar, saboda ƙwazon da suka nuna a fannin nazarin harshen Sinanci, a yayin wani biki da aka shirya a jami’ar Cape Coast (UCC) .

Da yake jawabi a yayin bikin jiya Jumma’a, jakadan ƙasar Sin dake ƙasar Ghana Lu Kun, ya bayyana fatan samun tallafin karatun, zai taimaka wa ɗaliban Ghana a dukkan matakai wajen yin fice a fannin nazarin harshen Sinanci.

Jakada Lu Kun ya bayyana cewa, yayin da ƙasar Sin ta zama ƙasa ta biyu mafi ƙarfin tattalin arziki a duniya, koyon Sinanci zai taimaka ba wai kawai wajen ƙarawa ɗaliban fahimtar ƙasar Sin ba, har ma da raba ra’ayin ci gaban ƙasar ta Sin da kuma cimma burin da suke fata.

Lu ya ba wa ɗaliban tabbacin cewa, a shirye ofishin jakadancin ƙasar Sin dake Ghana yake, wajen ba da taimako ga ‘yan Ghana masu son yin karatu a ƙasar Sin.

A nasa jawabin, mataimakin shugaban jam’iyyar UCC, Johnson Nyarko Boampong, ya ce muhimmancin koyon harshen Sinanci na daɗa ƙaruwa.

Fassarawar Ibrahim Yaya