Wakilin musamman na Xi zai halarci jana’izar Sarauniya Elizabeth ta biyu

Daga CMG HAUSA

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Mao Ning, ta sanar a yau Asabar cewa, bisa gayyatar da gwamnatin ƙasar Birtaniya ta yi masa, wakilin musamman na shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, kuma mataimakin shugaban ƙasar Wang Qishan, zai halarci jana’izar sarauniya Elizabeth ta biyu da za a yi a birnin Landan a ranar Litinin 19 ga watan Satumba.

Fassarawar Ibrahim

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *