Wang Yi ya yi tsokaci kan sakamakon Ziyarar Xi

By CMG HAUSA

Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya halarci taron majalisar shugabannin ƙasashen mambobin ƙungiyar haɗin gwiwar Shanghai karo na 22 a birnin Samarkand, tare da kai ziyarar aiki a ƙasashen Kazakhstan da Uzbekistan bisa gayyatar da aka yi masa, tsakanin ranakun 14 zuwa 16 ga wannan wata.

Mamban majalisar gudanarwar ƙasar kuma ministan harkokin wajen ƙasar Wang Yi, ya yi bayani kan ziyarar shugaban ga manema labarai.

Yana mai cewa, ziyarar da shugaba Xi Jinping ya yi, ita ce ziyara ta farko da ya kai zuwa ƙetare, tun bayan ɓarkewar annobar cutar COVID-19, don haka tana da ma’ana ta musamman, ra’ayin jama’ar ƙasa da ƙasa na ganin cewa, shugaba Xi ya zabi ƙasar dake tsakiyar nahiyar Asiya, domin yin ziyararsa ta farko, tun bayan bazuwar cutar, lamarin yana da babbar ma’ana, saboda ziyarar za ta ba da gudummowa ga ƙasar Sin, yayin da take ƙoƙarin daƙile yunƙurin ƙasar Amurka na hana ci gabanta, bisa taimakon aminai kasashen mambobin ƙungiyar haɗin gwiwar Shanghai, hakan ya nuna hikima da imani da hangen nesa na shugaba Xi.

Yana mai bayyana cewa, matsayin ƙasar Sin a duniya da tasirin da take yi a fadin duniya suna karuwa.

Wang Yi ya ƙara da cewa, yayin ziyararsa ta tsawon sa’o’i 48, shugaba Xi ya halarci ayyukan da aka shirya kusan 30, tare kuma da samun babban sakamako, ana iya cewa, ziyarar Xi ta ciyar da ƙungiyar haɗin gwiwar Shanghai gaba yadda ya kamata, kana ta sa ƙaimi da ci gaban hulɗar dake tsakanin ƙasar Sin da ƙasashen da abin ya shafa.

Mai fassarawa: Jamila

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *