Rundunar ‘yan sandan Kano ta baje kolin masu laifuka daban-daban 331

Daga BABANGIDA S. GORA a Kano

Kimanin mutum 331 ne rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta yi nasarar yin awon gaba da su kan laifuffuka mabambanta a jihar Kano cikin makonni huɗu.

Hakan ya biyo bayan lokacin da sabon kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano CP Abubakar Lawal Daura lokacin da yake gabatar wa da manema labarai masu laifin karo na farko bayan shafe makonni biyu da zuwansa matsayin Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar.

CP Abubakar Lawal ya ce cikin ikon Allah ana cigaba da samun nasara daga batun samar da zaman lafiya a Jihar Kano ta ƙoƙarin gwamnati jihar, kwamitocin unguwanninsu kan ɓangaren ‘yan sanda, masu hannu da shuni, masarautu, sauran jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki, inda ya yaba da irin gudunmuwar da ‘yan jarida suke ba wannan runduna dama sauran ɓangarori yana basu nasara.

Daura ya ce waɗanda aka kaman sun haɗa da ‘yan fashi da makami 51, ‘yan damfara 12, sai masu garkuwa da mutane don kuɗin fansa 69, masu safarar mutane mutum 7.

Sauran masu laifukan sun haɗa da masu satar motoci da mashinan adaidaita sahu su 18, sai ‘yan daba su kimanin 168, haka kuma rundunar ta yi nasarar kama waɗanda ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi su shida.

Kazalika an kuma kuvutar da mutune 11 daga hannun masu garkuwa da mutane da kuma mutanen da aka yi safara zuwa bautarwa wasu ƙasashen aikatau su 17.

An kuma gano bindigogi qira daban-daban har guda 48, motoci 24 da adaidaita sahu 12, mashina guda 2 sai wuƙaƙe guda 94, akwai kuma tabar wiwi ɗauri 306 da katan ɗin ƙwayar turamol guda 2.

Akwai kuma batiran motoci guda 30 da aka gano tare da tibin bango guda ɗaya, sai fankar sama guda 9, da injin markaɗe guda ɗaya, sai sholisho guda 48, akwai kuma ƙwayar Exol guda 1,2143 sai wayar hannu 75 da abin ɓalle ƙarfe kowane iri da kuma tarin ‘ya’yan makullai masu buɗe kowane abu.

Daga ƙarshe Kwamishinan ‘Yan Sandan ya yi kira ga jama’ar Jihar Kano da su ci gaba da taimkon jami’an tsaro wajen kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *