Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, da limamin cocin Emmanuel Chapel Methodist, Farfesa Konyinsola Ajayi, sun bayyana takaicin su kan taɓarɓarewar harkokin shari’a a Nijeriya, tare da bayyana hakan a matsayin abu na biyu mafi muni na cin hanci da rashawa a ƙasar.
Sanusi ya koka da cewa duk da cewa aikin alƙalanci a Nijeriya na da sarƙaƙiya saboda taɓarɓarewar harkokin siyasa, amma a wasu lokutan alƙalan na yanke munanan hukunce-hukunce.
A nasa ɓangaren Ajayi ya ce duk da cewa ya kamata ɓangaren shari’a ta zama tana tabbaci a Nijeriya, amma ita ce babbar hanya mara tabbas.
Sun yi wannan jawabi ne a Legas a taron ‘Tattaunawa da Jama’a kan Harkar Shari’a’, wanda ƙungiyar ‘Moɓement for Islamic Culture and Awareness’ (MICA) ta shirya domin bikin ƙarin girman mai shari’a Adewale Abiru zuwa Kotun ƙoli.
Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Alƙalin Alƙalan Nijeriya, Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun; tsohon gwamnan jihar Legas, Babatunde Fashola; Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi; Mataimakin Shugaban Jami’ar Legas (Deɓelopment Serɓices) Farfesa Ayodele Atsenuwa, Dokta Wale Babalakin da Farfesa a Kimiyyar Siyasa, Adele Jinadu.
A nasa jawabin, Sanusi, wanda ya bayyana ɓangaren shari’a a matsayin babban ɓangare mai ’ya’ya da yawa, ya ce a riƙa hukunta masu neman gurɓata ɓangaren.
Ya ce: “Gaskiya, a kowace ɓangaren, misali kamar a cikin gidan mutum ɗaya mai ’ya’ya da yawa, ana samun nagari, kuma a kan samu mutum ɗaya ko biyu na banza da suke lalata sunan dukka mutanen gidan. Kuma ina ganin yawancin maganganu marasa kyau da ake ji game da harkokin shari’a wani abu ne da ke da alaƙa da ’yan tsirarun alƙalai.
“Na haɗu da alƙalai da yawa na kirki, kuma dole ne in faɗi gaskiyar cewa ni da kaina ban haɗu da wani mugun alkali ba. Amma gaskiyar magana ita ce, “alƙalin alƙalai, kina da babban aiki”. Domin a ƙarshen rana, dukanmu dole ne mu yi yaƙi don tsaftace ƙasa. Don haka, idan akwai kaɗan marasa kyau, dole ne a magance su. Dole ne mu tabbatar da cewa mun rage adadin alƙalai marasa kyau baki ɗaya.”
Sarkin, wanda ya kuma buƙaci alƙalai da kada su kasance masu bayar da shawara ga masu aikata ba daidai ba, ya kuma roƙi masu gurɓata harkar shari’a don samun abin da su ke so da su daina.
