Babu wata barazana da za ta hana ni rusau a Abuja – Wike

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya ce gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba sakamakon zagon ƙasa daga wasu ƙungiyoyin farar hula da masu fafutuka a neman a dakatar da rusau a Abuja.

Ministan ya bayyana hakan ne biyo bayan ziyarar da ya kai unguwar Ruga da aka ruguje tare da shugabannin hukumomin tsaro a babban birnin tarayya Abuja, bayan wani taron majalisar tsaro da aka yi a yammacin Lahadi.

An rawaito cewa wasu daga cikin mutanen da aka rusa wuraren su tare da lauyan kare haƙƙin ɗan Adam, Deji Adeyanju, da kuma wani mai suka a shafukan sada zumunta, ɓincent Martins Otse, wanda aka fi sani da ɓeryDarkMan, a ranar Juma’a, sun nuna rashin amincewarsu da rusau ɗin da ma’aikatar kula da cigaban ƙasa ta yi, inda suka yi kira ga shugaba Bola Tinubu da ya gaggauta tsoma baki.

Wike ya ce “gwamnati na da haƙƙin kare rayuka da dukiyoyi a babban birnin tarayya Abuja da kuma tabbatar da cewa Abuja na ɗaya daga cikin birane mafi kyau a duniya.”

“Har ila yau, babu wani nau’i na zage-zage, barazana ko cin zarafi da zai dakatar da ni; dole ne mu zagaya don aiwatar da ayyukanmu.

“Muradinmu shi ne mu kare rayuka da dukiyoyi, mu kare Abuja ta yadda za ta kasance ɗaya daga cikin birane mafi kyau a duniya,” inji shi.

Ministan ya buƙaci mazauna yankin da kada su sake gina wani gini a yankin, na wucin gadi ne ko na dindindin har sai gwamnati ta yanke shawara, ya ƙara da cewa za a ruguza wasu gidajen kwana da ke faɗin birnin tare da mayar da su sabbin tashohin motocin bas domin samun tsari.

“Game da wannan hanyar, mun gaya musu babu wanda zai gina wani abu, na wucin gadi ko na dindindin. Ba za mu kyale su ba har sai gwamnati ta yanke shawara ta ƙarshe kan abin da za ta yi kan wannan fili.

Wike ya kuma ba da umarnin cewa wakilai biyar na mazauna yankin su gana da shugabannin hukumomin tsaro da daraktocin kula da filaye da raya ƙasa, don ba da shawarwari ga gwamnati kan abin da ya kamata a yi.

Da yake jawabi tun da farko, mai magana da yawun yankin, Abba Garu, ya roƙi ministan da ya samar musu da matsuguni, yana mai cewa aikin rusau ɗin na baya-bayan nan da aka gudanar a makon da ya gabata ya sanya gwamnatocin da suka shuɗe suka rusa karo na 22.

By ukarofi