Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Mai Martaba Sarkin Gusau, Alhaji Dr. Ibrahim Bello OFR, ya bada tabbacin goyon bayansa ga masu yiwa Ƙasa hidima da aka turo Jihar Zamfara a kowane lokaci.
Da yake jawabi a lokacin da yake karɓar tawagar NYSC ƙarƙashin jagorancin kodinetan jihar, Sarkin ya nuna jin daɗin sa da ziyarar inda ya bayyana cewa a shirye yake ya ba da taimako ga shirin a duk lokacin da ake buƙata.
Sarkin ya buƙaci masu hidimar da su ɗauki jihar Zamfara a matsayin tamkar a gidansu suke .
Sarkin ya kuma ƙara jan hankalin masu hidimar da su yi la’akari da zama a jihar Zamfara bayan shekarar hidimar su, inda ya ce, “Bayan hidimar, idan har kuka yanke shawarar zama a nan, muna maraba da ku.
Ya miƙa goron gayyata ga masu hidima maza da mata, inda ya kara da cewa mata na iya tunanin yin aure a jihar.
Tun da farko a nasa jawabin, Ko’odinetan NYSC na jihar Zamfara, Mallam Muhammad Lawan Ahmed, ya bayyana jin daɗin sa ga masu yiwa Ƙasa hidimar bisa irin karramawar da su kayi ma masautar ta Gusau.
Ya bayyana cewa ziyarar na ɗaya daga cikin ci gaba da hulɗa da masu ruwa da tsaki a jihar tun bayan hawansa ofis domin tabbatar da inganta tsaro da walwalar masu yiwa Ƙasa hidima.
Mallam Ahmed ya yabawa gwamnan Jihar Zamfara kan yadda ya duba alawus alawus ɗin masu hidimar, sannan ya roƙi sarkin da ya miƙa godiyar su ga gwamnan idan ya gana da shi.
“Muna da masu yiwa Ƙasa hidima da ke shigowa Jihar Zamfara daga jihohin tarayya daban-daban, a yau sun zo gaishe ka, mu ‘ya’yanku ne, muna ƙarƙashin kulawar ku, muna godiya da ku da kuka ba mu damar yin mu’amala da ku.” Ya jaddada.
