Sarkin Kano ya ƙaddamar da kwamitin bikin shekara 90 da KOFA ta tsara yi a 2025

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano         

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya kaddamar da kwamitin shirye-shiryen bikin cika shekara 90 da kafuwar makarantar firamare ta Kofar Kudu, wace aka kafa a 1935 a gidan Sarkin Kano wanda qungiyar tsofaffun dalibai wato Kofar Kudu Old Pupils Primary School, (KOFA) karkashin shugabancin Kwamared Abubakar Shehu Kwaru ke shirin aiwatarwa da bikin a 2025 idan Allah ya kaimu lafiya.

Kamar dai yadda Sarkin Kano ya kaddamar da wannan kwamiti a lokacin taron kungiyar na shekara 50 da dalibai karkashin shugabancin Alhaji Yusuf Aliyu Yakasai,  ya aji na shekarar 1972 wanda shima Sarkin Kano dan wannan kungiyar ne ta aji na 72 kamar dai yadda shi shugaban aji 72 ya tabbatar a wurin taron wanda ya gudana a harabar makarantar a ranar Litinin da ta gabata a Kano.

Tun da farko a jawabin sa sarkin kano Alhaji Aminu Ado bayero Kan ganin wannan ranar mai tarihi inda kuma ya yabawa tsoffafun daliban na KOFA kan shirya wannan taro na wannan rana’a da kuma bikin shekaru 90 na kafuwar wannan makarantar tamu inda kuma ya hora daliban da sauran al’umma kan taimakawa harkar ilimi da al’umma baki daya.

Ita kuwa shugabar makarantar Hajiya Malama Hauwa Habib Sarki yaba wa Maimartaba Sarkin Kano ta yi kan karrama su da ya yi wajan tsawa tsayin daka na ganin an samu nasara a wannan biki musamman ganin irin yadda wannan makaranta ta samu gudummwar daga tsoffafin dalibai wanda ta bukaci sauran dalibai na wannan makaratarsu su kafa qungiyoyi don koyi da shugaban dalibai aji na 72 da kuma shugaban kungiyar na kasa Kwamarad Abubakar Shehu Kwaru kamar yadda Bashir Adamu Kafinta Kofar Nassarawa, wanda aka fi sani da Wambai Kafinta, daya daga cikin dimbin daliban da suka halarci taron cika shekara 50 da kammala makarantar su ya yaba wa shugabannin KOFA a inda Hajiya Umma Dauda Rola Shugabar Makarantar firamare Kimiyya ta Kurmawa wa ce ta bayyana farin cikinta da wannan taro a  wannan rana.

By Editor