Matatar Fatakwal za ta fara aiki bayan shekaru

Spread the love

*Tinubu ya bada umarni maido da tsarin ciyar da dalibai

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Matatar mai fetur ta Fatakwal da ke Jihar Ribas za ta sake fara aiki bisa alqawarin da Gwamnatin Tarayya ta yi na tabbatar da samar da tace kayan a cikin gida a watan Disamba na 2023.

Cigaban yana zuwa ne bayan shekaru da yawa da rufe matarar da kuma gyara kayan aikinta. Uku daga cikin matatun mai na Nijeriya a Fatakwal, Warri da Kaduna su na da qarfin tace ganga 445,000 a kowace rana, amma an rufe su tun a shekarar 2019.

Sai dai kuma a watan Agusta, Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Sanata Heineken Lokpobiri, ya ce, matatar man za ta koma aiki a Disamba.

Lokpobiri ya bayyana hakan ne a yayin wani rangdin da ya kai ziyarar gani da ido a kan cigaban aikin gyaran matatu da aka yi a kamfanin PHRC.

“Manufarmu ta zuwa nan a yau ita ce mu tabbatar da cewa nan da ‘yan shekaru masu zuwa, Nijeriya ta daina shigo da mai. Daga abin da muka gani a nan a yau, matatar Fatakwal za ta fara aiki a karshen shekara,” inji shi yayin ziyarar.

Sake gudanar da ayyuka a matatar mai ta Fatakwal ya zo ne bayan shekaru biyu da gwamnatin tarayya ta amince da kashe dala biliyan 1.5 (Yuro biliyan 1.2), domin gyara daya daga cikin manyan matatun mai.

Gwamnati ta zabi wani kamfani mai suna Maire Tecnimont dan Kasar Italiya, don gudanar da aikin gyara a ginin Fatakwal wanda ke da karfin tace ganga 210,000.

A wani labarin kuwa, Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya bayar da umarnin sake maido da tsarin ciyar da daliban makaranta domin magance kalubalen rashin zuwan yara makaranta.

Tsohon Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari ne ya dakatar da tsarin bayan shafe shekaru a na tafiyar da shi.
Sai dai a yanzu shugaba Tinubu ya ba da umarnin a farfado da tsarin saboda zai taimaka wajen magance matsalolin da suka shafi ilimi.

Ya ce, idan ba a magance matsalar ba, zai yi matukar wahala a iya rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.
Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman ne ya bayyana haka a wani taron yini daya da aka yi.

Ministan ya ce, an yi taron ne domin samar da hanyoyin aiwatar da dukkanin tsare-tsaren da za su magance duk wasu kalubale da kuma yadda hukumomi daban-daban za su taimaka wajen rage matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta.

By Editor