Daga BASHIR ISAH
An yi kira ga al’ummar Nijerya da su hade kai wajen yaki makiya cikgaban kasa a wannan lokuci na bukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.
Babban Hafsan Tsaron Kasa, Janar Christopher Musa ne ya yi wannan kira a cikin sakon taya murna da ya fitar a ranar Lahadi mai dauke da sa hannun Mukaddashin Daraktan Yada Larabai na rundunar soji, Birgediya Janar Tukur Gusau.
“Yayin da muka bi sahun masu bikin Kirsimeti da sabuwar shekara a fadin duniya, ina yabo ga Sojojin Nijeriya da ’yan Nijeriya bisa jajircewarsu. Da fatan alherin da ke tattare da wannan lokaci ya ci gaba da hade kanmu har bayan zuwa bayan wanan lokaci.”
Haka nan, Babban Hafsan ya kuma yi amfani da wannan dama wajen kira ga ’yan Nijeriya da su ci gaba da bai wa sojoji goyon baya domin karfafa musu gwiwa wajen ci gaba da bai wa kasa kariya.”
Ya kara da cewa, “yayin da muke ban-kwana da wannan shekarar, muna fatan shiga sabuwar shekara da sabon fata. Tare da gudummawar ’yan Nijeriya za mu kai gaci wajen bai wa kasarmu kariya.
