Mutum 11 sun mutu a hatsarin mota a Jigawa

Daga BASHIR ISAH

Akalla mutum 11 ne aka rawaito sun riga mu gidan gaskiya a ranar Asabar da ta gabata sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da su a yankin Kwanar Gujungu da ke Karamar Hukumar Taura a Jihar Jigawa.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Jigawa, ASP Lawan Shiisu, shi ne ya tabbatar da aukuwar hakan jiya Lahadi a Dutse, babban birnin jihar.

Shiisu ya ce hatsarin ya auku ne a ranar Asabar da misalin karfe 12:00 na rana, inda wata mota kirar Honda saloon mai lamba NSR 469 AE da wata kirar Golf wagon mai dauke da lamba AUY 292 XA, suka yi taho mu gama.

Jami’in ya ce, jami’ansu na ofishin yankin Taura ne suka garzaya inda hatsarin ya auku inda suka kwashi wanda lamarin ya rutsa da su zuwa Babbar Asibitin Taura, wanda a nan likita ya tabbatar da mutuwarsu.

Ya kara da cewa, bincikensu ya gano motar Honda mai dauke da pasinja 5, sunan direban Abdullahi Muhammad, yayin da direban Golf wagon mai dauke da pasinja 4, sunansa Safiyanu Mamu.