Ta yaya za ki kula da fatarki a lokacin sanyi

Daga AISHA ASAS

Yayin da aka ce sanyi ya karato, mutane da yawa suna tausayawa halin da fatarsu za ta shiga yayin da suka yi arangama da yanayin na sanyi.

A lokacin sanyi fata na yamushewa saboda yanayin iskar hunturu, kuma yakan yi muni musamman ga wadanda ba su san yadda za su ba wa fatar tallafi ba.

Yanayin sanyi ba iya fata ya tsaya ba, domin hunturu na tava lafiyar gashi, ta hanyar yawan karyewa, sai kuma uwa uba kaushi ko fasau da kafa ke yi.

Wadannan matsalolin na lokacin sanyi na sauya fasalin jiki tare da sanya shi damuwa, har ta kai kwalliya ma ba ta cika fita radau yadda ake so ba a lokutan sanyi.

Matakan da ya kamata ki dauka a lokacin sanyi:

A guje wanka da ruwa masu zafi: na san mai karatu zai iya cewa hakan ba mai yiwa ba ne, kasancewar ya zama al’ada da muke yi a duk lokacin da aka ce sanyi ya yi sallama.

Sai dai abinda ba ku sani ba shi ne, wanka da ruwan zafi na daya daga cikin ababe masu bayar da gudunmuwa ga lalacewar fata. Don haka idan ya zama dole amfani da ruwan zafi, to a yi da masu dumi.

Yawaita shafa mai: idan muka kalli yanayin yadda lokacin hunturu yake kasancewa na daga iska da ke saurin busar da jiki da kuma sanyin wanda ke daskare abokanin tafiyar fatar, za mu ga cewa, kusan kodayaushe fatar tana kokarin bushewa ne, hakan ke sa irin shafar da ka ke yi masa a baya ba zai wadatar ba.

Don haka yake da muhimmanci yawaita shafawa fatar mai. Kuma idan za a hada man shafawa na lokacin sanyi, yana da kyau a hada shi da mai ruwa-ruwa, wato lotion, saboda yana taimakawa fata wurin jika ta.