Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Mai martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmummuni Kabir Usman ya ce Arewa ba za ta taɓa komawa yadda take ba sai al’umma da shugabanni sun so junan su tare da haɗa kai wajen cigaban yankin.
Sarkin ya faɗi haka a lokacin da sabon Maraɗin Katsina Hakimin kurfi Ach Mansir Ahmadi kurfi da tawagarsa su ka kaiwa sarkin ziyarar godiya a fadar Sarkin.
“Allah na tare da mu idan muka ƙaunaci junan mu, kuma mu aikata alheri” inji sarkin.
Ya bayyana ƙasar Kurfi a matsayin gidan sa na biyu kuma shi marigayi Maraɗin Katsina mutum ne fitacce da ya riƙe al’ummar sa bisa amana .
Sarkin ya jawo hankalin sabon hakimin da ya riƙe al’ummar sa bisa amana a ko da yaushe buƙatar su ke kan gaban sa.
Ya kuma yi kira ga shugabanni da su ji tsoron Allah wajen jagorancin al’ummar su da tunatar da su cewa duniya ba wajen zama bane.
Tunda farko shugaban tawagar Galadiman Katsina Hakimin Malumfashi mai shari’a Sadiq Abdullahi Mahuta ya nuna jin daɗin sa ga yadda masarautar Katsina ta dawo da martabar ta wajen naɗa waɗanda suka dace da Sarauta.
Ya ƙara da cewa,dama sarkin Katsina Abdulmummuni Kabir Usman ya san ƙwarewa da cancanta na sabon Maraɗin Kurfi.
Tunda farko, wanda yayi magana a madadin yan’uwa da abokan sabon Maraɗin,Magajin Tamawa Alhaji Shehu Sani yace,sun zo fadar mai martaba suyi godiya bisa sarautar da aka ba ɗan uwansu.
Sai yayi addu’a “Allah tsare sarki da masarautar Katsina da kuma sabon hakimin”.
Magaddai da masu unguwanni da sauran al’umman ƙaramar hukumar Kurfi suka raka sabon Maraɗin Kurfi zuwa fadan mai martaba sarkin Katsina.