Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Na fara karanta labarin ‘Tattaki Cikin Zamunna’ wanda Farfesa Yusuf Muhammad Adamu na Jami’ar Bayero ta Kano ya wallafa ne tun a tsohuwar jaridar Nasiha wacce ake bugawa a Kaduna, wacce a lokacin take tsakuro labarin ana bugawa mako-mako. Kodayake a lokacin ina makaranta, ban yi zurfi wajen nazarin ilimin ‘Time Traɓel’ sosai ba. Sai dai salon marubucin na ƙirƙirar labari da salon rubutu na ‘Science Fiction’, wanda ba kasafai za ka ga irin sa a rubutun ‘yan Afirka ba, ballantana ma a yi batun marubutan Hausa, ya daki tunanina sosai. Har yanzu idan na ɗauki labarin ina karantawa saboda ingancin rubutun yana min kamar sabon labari ne. Ina jin ni dai har kawo yanzu ban san wani littafi da aka rubuta shi da irin wannan salon ba.
Irin wannan labari ne, yake ɗaukar hankalin ƙwararrun manazarta na duniya, saboda irin zurfin bincike da kaifafa tunani da ake kimsawa a cikinsa, saɓanin yadda muka saba rubuta labari, irin na nuni cikin nishaɗi ko hannunka mai sanda.
Babu shakka labari mai inganci da aka rubuta shi bayan dogon nazari da bincike, yana da tasiri na daban, ba a wajen manazarta kaɗai ba har ma da masu karatu. Shi ya sa marubuta na jiya da wasu daga cikin masu koyi da su a yanzu, suka zama gagarabadau kuma madubi a wajen sauran marubuta.
Duk da kasancewar marubutan yammacin duniya, sun yi nisa sosai a wannan fage na rubutun ƙirƙirarren labarin kimiyya (Sci-fi), a karon farko bayan tsawon shekaru cibiyar nazari da shirya gasar fitattun littattafai ta duniya ta Booker Prize Award ta zaɓi littafin ‘Orbital’ wanda marubuciya Samantha Harvey ‘yar ƙasar Birtaniya ta wallafa. Sakamakon salon da marubuciyar ta yi amfani da shi mai jan hankali, wanda kai tsaye bai nuna ƙirƙirarren labarin kimiyya ba ne, amma ya yi ninkaya a duniyar sararin samaniya, wajen bayyana wata rayuwa da wasu ‘yan sama jannati su shida suka yi.
Littafin Orbital, wanda aka rubuta shi da harshen Turanci, yana da shafuka 136, kuma yana ƙunshe ne da labarin wasu masu ilimin binciken sararin samaniya su shida da suka fito daga ƙasashen Amurka, Ingila, Italiya, Rasha, da Japan, waɗanda suka tafi wani bincike a duniyar wata, amma sai suka riƙa ta’ajibin yadda rayuwa take a wannan duniyar tamu. A yayin da suke cikin na’urar su da ke aiki da ita, sun kewaya duniya sau goma 16 a cikin wuni guda, inda aka bayyana na’urar da suke ciki tana gudun mil dubu 17 a kowacce awa ɗaya.
Daga cikin na’urar tasu, sun riƙa kallon yadda halittar duniya take cike da mamaki, yadda wasu wuraren ake cikin rana, wasu na cikin dare, wani wajen na cikin ambaliyar ruwa wani wajen na fuskantar fari, wani wajen na zaune lafiya, wani wajen ana ta rugugin bama-bamai, yayin da kuma dukkansu ke ƙunshe cikin wata dunƙulalliyar duniya guda ɗaya. Duk da irin bambance-bambancen ƙasashen da suka fito, da siyasa da al’adun da suka raba su, wannan shawagi nasu ya tabbatar musu da cewa ɗan’adam halitta ce guda ɗaya.
Marubuciyar littafin, Samantha Harvey, ta fara tunanin rubuta labarin ne a lokacin annobar COVID-19, inda aka kulle mutane a gida na tsawon watanni, saboda yaƙi da yaɗuwar cutar. A lokacin ne ta yi ta nazari kan littattafai da finafinai, da ayyukan ƙwararru akan yadda rayuwa a sararin samaniya take. Don haka bayan nazarinta ta fara aiki kan wannan sabon labari, da ta yi shi da nufin auna yadda ɗan’adam zai samu kansa a wata duniya, da yadda bincikensa zai bayyana masa muhimmancin da duniyarsa ke da shi, ya kuma gane hakkin ba da gudunmawa ga cigabanta da kare muhallinta daga gurɓacewa, da kare rayukan da ke rayuwa a ciki ta, a maimakon halaka su.
Wannan littafi na ‘Orbital’, duk da kasancewar sa mafi ƙanƙanta cikin littattafan da aka tantance kuma aka duba, ya zo da wani salo da ya ja hankalin alƙalan gasar da a ƙarshe suka amince shi ne ya fi cancanta. Saboda irin saƙon da yake ɗauke da shi ga al’ummar duniya, wanda ke koyawa jama’a muhimmancin girmama juna da kawar da wariya da bambance-bambance, da yaƙe-yaƙe, waɗanda ke lalata zamantakewa a duniya.
‘Orbital’, shi ne littafi na biyar da marubuciya Samantha Harɓey ta rubuta, da suka shafi ƙirƙirarrun labarai, a cikin littattafai shida da ta wallafa. Sakamakon nasarar da ta samu ta zama gwarzuwar marubuciya ta shekarar 2024, Gidauniyar Gasar Booker Prize ta Ingila ta ba ta kyautar Fam dubu 50, tare da karɓar kambun gasar na bana daga hannun gwarzon shekarar da ta gabata Paul Lynch.
Manufar yin wannan dogon sharhi da nake yi wanda ya shafi fitattun littattafan turawa shi ne mu fahimci cewa, mu ma muna da damar da za mu iya yin rubutu masu muhimmanci da tasiri da zai shafe tsawon zamani ana amfana da su, kuma duniya tana jinjinawa zurfin tunanin da aka yi wajen tsara labaran.
Koƙarin da ƙungiyoyi da cibiyoyin ilimi ko ma’aikatu suke yi wajen sanya gasa domin zaburar da marubuta zuwa ga yin bincike da nazari mai zurfi, yana taimakawa ainun, inda ake samun jajirtattun marubuta da ke fitar da labaru masu tasirin gaske, waɗanda a ko’ina za a iya gogayya da su. Kodayake a gaskiya irin waɗannan cibiyoyi sun yi ƙaranci sosai a Najeriya ta Arewa, in ka cire gasar Gusau Institute da ake shiryawa, wacce ke fitar da littafi guda sukutum. Sai kuma na baya-bayan nan wanda Gidauniyar Open Arts ta ɗauki nauyin buga littattafan marubuta mata daga Arewa, waɗanda aka rubuta da harshen Hausa da Turanci. Sauran masu shirya gasannin akasari ta gajeren labari suke shiryawa, a maimakon ta littafi.
A shekarar 2023, an fitar da wasu littattafai da suka samu nasarar zama na ɗaya da na biyu daga cikin jerin littattafai 13 da suka yi zarra a gasar Gusau Institute, waɗanda salonsu ya burgeni sosai, kuma nake ganin za su iya shiga irin matakin da marubutan turanci suke fafatawa akai, duk da yake dai akwai sauran aiki, idan aka duba ɓangaren gwanancewar rubutu.
Littafin ‘Wata Duniya’ na Ruƙayya Ibrahim Lawal daga Jihar Sakkwato, da ‘Harin Gajimare’ na Hauwa Shehu daga Jihar Kano, sun fito da wani salon labari da ba kasafai marubutan mu na Hausa suke fito da irin sa ba, sai ɗai-ɗai. Idan a ce wannan cibiya ta Gusau Institute da ire-irenta, za su dage akan wannan salon nata, su kuma yi tsayin daka wajen ƙarfafa gwiwar marubuta wajen fitar da salon labarai, masu buƙatar zurfin bincike da nazari, babu shakka za a samu juyin juya hali sosai, wajen inganta tsarin rubutun Hausa.
Babu mamaki shi ya sa har yanzu labarin ‘Tattaki Cikin Zamunna’ yake cigaba da zama abin kwatance, idan ana labarin salo na badalla tunanin mai karatu, da siddabarun ba da labari, wanda mai karatu bai taɓa kai hankalinsa wajen ba.