Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya musanta rahotannin da ke yawo cewa ya bayyana goyon bayansa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin ya sake tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Bashir Adefaka, ya fitar, an bayyana rahotannin a matsayin ƙarya da kuma masu yaudara, tare da jaddada cewa Sarkin Musulmin ba shi da wani ɗan takarar da yake marawa baya a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Sanarwar ta ce matsayinsa na jagoran addini da na gargajiya, kuma uba ga dukan ‘yan Nijeriya, ba ya ba shi damar nuna son kai ko shiga siyasar jam’iyyun ƙasa.
Ta ƙara da cewa Sarkin Musulmin ba shi da wani ɗan takara da ya fi so, kuma ba zai goyi bayan kowane mai neman takara ba, a bainar jama’a ko a ɓoye.
Sanarwar ta ce: “Hankalin tawagar yaɗa labaran Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya kai kan wani rahoto da ke yawo a wasu kafafen sada zumunta, wanda ke ƙoƙarin nuna cewa Sarkin Musulmi ya buƙaci ‘yan Nijeriya su goyi bayan sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.
“Amsarmu a taƙaice ita ce, hakan ba zai yiwu ba, domin Sarkin Musulmi uba ne ga kowa, kuma ba zai furta irin wannan magana ba, a fili ko a wani wuri.”
Sanarwar ta bayyana cewa matsayin Sarkin Musulmi ya wajabta masa kasancewa tsaka-tsaki da kuma karɓar kowa ba tare da la’akari da jam’iyyarsa ko ra’ayinsa na siyasa ba.
Ta kuma ce ofishin da yake riƙe da shi yana buƙatar cikakken adalci da rashin nuna son kai, don haka bai dace ya goyi bayan wani ɗan takara kafin babban zaɓen ƙasa ba.
Haka kuma, sanarwar ta bayyana rahotannin da ke alaƙanta Sarkin Musulmi da yaƙin neman zaɓen Tinubu na 2027 a matsayin mugun nufi daga wasu masu son cimma muradunsu na kashin kai ta hanyar jefa sunan Sarkin Musulmi cikin siyasar jam’iyyu.
A cewar sanarwar, waɗannan iƙirarin ba su dace da tarihin Sarkin Musulmi na adalci, haɗin kai da kuma rungumar kowa ba.
Sarkin Musulmin ya kuma sake tabbatar da cewa zai ci gaba da karɓar baƙuncin dukan ‘yan Nijeriya, ciki har da shugabannin siyasa da masu riƙe da muƙaman gwamnati, ba tare da hakan yana nufin yana mara wa wani baya a siyasance ba.
“ƙofofin Sarkin Musulmi a buɗe suke ga kowa, ba tare da la’akari da jam’iyyarsa ko ra’ayinsa na siyasa ba. Mai Alfarma ya kasance uba ga kowa, kuma zai ci gaba da mu’amala da dukan ‘yan Nijeriya cikin adalci da rashin nuna bambanci,” inji sanarwar.
