Sauraren Ƙararrakin Zaɓe: Kotu ta ɗage zamanta zuwa ranar Talata

Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa mai zamanta a Abuja, ta ɗage zamanta zuwa ranar Talata.

Yayin zamanta na gaba, ana sa ran Kotun ta saurari ƙorafin da Atiku Abubakar da jam’iyyar APM suka shigar ne game da zaɓen na Shugaban Ƙasa.

Sannan ta saurari ƙararrakin da Jam’iyyar Labour da APP da kuma Peter Obi suka shigar a ranar Laraba.

Duka ƙararrakin da aka shigar suna ƙalubalantar sakamakon zaɓen Shugaban Ƙasa da ya gudana ne a ranar a ranar 25 ga Fabraru.

Zaɓen da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta tabbatar da Bola Tinubu ma Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara bayan da ya samu ƙuri’u 8,794,726, kana babban abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya samu ƙuri’u 6,984,520, sannan Peter Obi ya rufa musu baya da ƙuri’u 6,101,533.

Rashin gamsuwa da sakamakon zaɓen ya sa Atiku da Obi suka garzaya Koton Sauraren Ƙararrakin Zaɓe don ƙalubalantar nasarar Tinubu.

A ranar Litinin Kotun, ƙarƙashin Mai Shari’a Haruna Tsammani ta fara sauraren ƙararrakin zaɓen.