Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
’Yan Nijeriya da sauran manazarta harkokin siyasa na ganin yadda ’yan siyasar ƙasar nan musamman gwamnoni, sanatoci, ’yan majalisu, da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa ke tururuwar canjin sheƙa daga jam’iyyun da aka zaɓe su akai zuwa jam’iyyar APC mai mulki, ko wasu manyan jam’iyyun adawa, alamu ne dake nuna cewa Nijeriya ta doshi zama ƙasa mai jam’iyya ɗaya, a wani ɓangare na shirye-shiryen tunkarar Babban Zaɓen shekarar 2027.
A halin yanzu, ana ganin tsarin dimukraɗiyyar Nijeriya na fuskantar sauyi mafi girma, inda jam’iyyu da dama ke rasa ƙarfinsu, wanda hakan ke haifar da tambayoyi a tsakanin ’yan Nijeriya. Ba da jimawa ba mun ga yadda wasu daga cikin gwamnoni musamman daga jihohin kudancin ƙasar nan suna sauya sheƙa daga jam’iyyu daban-daban zuwa babbar jam’iyyar APC. Misalin hakan akwai Gwamnan Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, wanda ya jima yana cikin APC, amma yanzu ya samu ƙarfafa gwiwa da goyon bayan al’ummar jiharsa, yayin da Gwamnan Jihar Ebonyi, Daɓe Umahi, ya bar jam’iyyar PDP zuwa APC. Haka kuma, mun ga yadda Gwamnan Jihar Ribas Siminalayi Fubara da Gwamnan Jihar Taraba Agbu Kefas, cikin wannan mako, suka canza sheƙa a wani yanayi mai ban mamaki. Wannan sauyi, mai kama da guguwar tsunami, na ƙara tabbatar da cewa APC na ƙara ƙarfi, yayin da jam’iyyun adawa ke fuskantar naƙasu.
A lokacin da Ifeanyi Okowa, tsohon Gwamnan Jihar Delta kuma mataimakin Atiku Abubakar a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, ya koma jam’iyyar APC, an samu cece-kuce sosai a ƙasar nan. Kaɗan ne daga ’yan Nijeriya suka yi tsammanin babban jigo kamar wannan daga babbar jam’iyyar adawa zai yi canjin sheƙa a wannan lokaci, musamman idan aka yi la’akari da yadda ‘yan siyasa daga matakai daban-daban ke barin jam’iyyunsu suna shiga APC.
Wannan lamari ya zama babban ƙalubalen da jam’iyyar PDP ta taɓa fuskanta a tsawon tarihin kafuwarta. Abin mamaki ne ƙwarai ganin yadda wasu daga cikin jihohin da aka san gida ne ga jam’iyyar PDP, duk yadda guguwar siyasa ta kai ga murɗawa, kamar irin su Akwa Ibom, Ribas, Taraba, Enugu har ma da Bayelsa, jihar da tsohon Shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya fito, sai gashi suna cigaba da faɗawa hannun jam’iyyar APC. Ga kuma Jihar Filato nan da itama ta daɗe a hannun PDP ta fara tangal-tangal, har ana raɗe-raɗin gwamnan jihar Caleb Mutfwang shi ma yana tattaunawa kan batun komawarsa APC, jam’iyyar da yanzu tsohon abokin adawarsa a lokacin zaɓen Gwamna na 2023, Farfesa Nentawe Yilwatda, yake shugabanta.
ɗaya daga cikin manyan dalilai shi ne sha’awar samun tallafi da goyon bayan gwamnatin tarayya domin bunƙasa jihohinsu ko aljihunsu. Wasu na ganin cewa shiga jam’iyya mai mulki na kawo sauƙi wajen samun abubuwan more rayuwa, samun tagomashi a wajen shugaban ƙasa, da samun sauƙin cin zaɓe a lokacin Babban Zaɓe mai zuwa. Haka kuma, rashin tsari da rikice-rikice a cikin jam’iyyun adawa na sa ‘yan siyasa su rasa kwanciyar hankali, kamar abubuwan da muka ga suna faruwa a jam’iyyar PDP.
Manazarta harkokin siyasa na ganin cewa hakan dake faruwa yana da tasa fa’idar, daga ciki akwai samar da natsuwa da tsari a harkar siyasa. Lokacin da jam’iyya guda ke da mulki, ana samun dagewa wajen aiwatar da manufofi cikin tsari ba tare da tsangwama daga masu adawa ba. A misali, ƙasar Sin ta nuna yadda tsarin jam’iyya guda ya taimaka wajen samun cigaba cikin hanzari. ƙasar Sin tana amfana da tsarin siyasar jam’iyya ɗaya, wanda hakan ya sa ƙasar ba ta samun ruɗanin siyasa irin na wasu ƙasashe, saboda adawar siyasa, tana samun tsari da cigaba mai ɗorewa.
Shugaban ƙasar Sin, ɗi Jinping, yana mulki da ƙarfin iko irin na sarakuna, ba tare da tsangwama daga majalisa ko ‘yan adawa ba. Wannan yana ba shi ikon yanke shawara cikin sauri, ba tare da samun tsaiko daga majalisa ba. Haka nan yayin ɗaukar mataki na aiwatarwa, ana samun damar gudanar da ayyuka cikin inganci, kuma akan lokaci. Ana ganin hakan na daga cikin dalilan da suka bai wa ƙasar Sin damar zama babbar ƙasa, da ta tashi daga ƙasa mai raunin tattalin arziki zuwa mai ƙarfin tattalin arziki na biyu a duniya. Ba ma fatan ganin Nijeriya na bin irin wannan tsarin kama-karyar na ƙasar Sin. Duk da yake wasu manazarta na yi wa tsarin da Shugaba Tinubu yake ƙoƙarin ɗora ƙasar nan akai, kallon kwaikwayon tsarin dimukraɗiyyar ƙasar Sin, mai jam’iyya ɗaya.
Sai dai kuma bin irin wannan tsari yana rage ingancin dimukuraɗiyya, a cewar masana harkokin siyasa. Suna ganin rashin adawa mai ƙarfi a siyasance na nufin ba a samun cikakken tsarin sa’ido kan yadda ayyukan gwamnati ke tafiya, wanda hakan zai iya hana shugabanni yin abubuwan da za su inganta rayuwar al’umma. Haka zalika, hakan na tauye ’yancin faɗin albarkacin baki da kuma kawo tsangwama ga ‘yancin dimokuraɗiyya.
Nijeriya na buƙatar cigaba da ƙarfafa jam’iyyun siyasa na ’yan adawa masu ƙarfi, domin tabbatar da shugabanci mai inganci da adalci. Lallai yawan canjin sheƙar ‘yan siyasa daga jam’iyyun adawa zuwa jam’iyyar APC na iya kawo naƙasu ga dimukraɗiyyar ƙasar nan. Saboda haka, ya zama dole a samar da tsarin da zai bada dama da goyon baya ga dukkan ɓangarori da ra’ayoyin ’yan siyasa daban-daban.
Duk da cewa gwamnatin tarayya na ƙoƙarin haɗa kan jam’iyyu, domin tabbatar da zaman lafiya da cigaban ƙasa, ya kamata a kiyaye dimukraɗiyyar Nijeriya wacce ta dogara akan ’yancin ra’ayoyin jam’iyyu daban-daban da fafutukar cin moriyar jama’a. Canjin sheƙar manyan ‘yan siyasa zuwa jam’iyyar APC na iya kawo ƙarancin adawar siyasa, wanda hakan zai jefa dimukraɗiyyar mu cikin barazana.Tabbas, ƙarancin jam’iyyun adawa a siyasa na rage armashin siyasa, da kuma rage ingancin mulki, domin babu wanda zai sanya ido sosai a aiki da manufofi. Saboda haka, akwai buƙatar sakewa ýan adawa mara su gudanar da harkokin su da ba su saɓawa doka ba, kuma a ƙyale ƙananan jam’iyyu su tafiyar da harkokin su yadda dimukraɗiyya ta basu dama, domin tabbatar da adalci da shugabanci nagari.
A ƙarshe, lallai ya kamata mu sani cewa ‘yancin walwala a tsarin dimukuraɗiyya bai tsaya kawai a samun jam’iyyu masu yawa ba, ko ba da ƙarfi a jam’iyyar siyasa guda ɗaya ba. Amma a samar da sahihin zaɓe da zai zama karɓaɓɓe ga kowanne ɓangare, da samar da kyakkyawan shugabanci da zai kare haƙƙin kowa. Mu yi hattara kada mu bari dimukuraɗiyyar Nijeriya ta zama tsarin jam’iyya guda, ko mu zama abin dariya ga wasu ƙasashe, domin dimukraɗiyya tana buƙatar gogayya da juna adawa mai ƙarfi, domin karfafawa jama’a gwiwa.
