Sharhi: Afirka wani babban dandalin haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa ne ba fagen takara tsakanin manyan ƙasashe ba

Daga LUBABATU LEI

Kwanan nan, sakataren harkokin wajen ƙasar Amurka Antony Blinken ya kawo ƙarshen ziyararsa a wasu ƙasashen Afirka guda uku.

A yayin ziyararsa a ƙasar Afirka ta kudu, Mr.Blinken ya gabatar da jawabi dangane da sabbin tsare-tsaren ƙasar Amurka a kan Afirka, inda ya furta cewa, duk da ja-in-jan da ke kara ta’azzara a tsakanin Amurka da sauran manyan ƙasashen irin su Sin da Rasha, Amurka dai ba za ta bukaci ƙasashen Afirka su zabi wani matsayin da za su dauka ba.

Duk da haka, Blinken ya yi ta furta “barazanar” da Sin da Rasha ke haifarwa a kalamansa.

Sai dai tuni ɓangarori daban daban a ƙasashen Afirka sun gane ainihin abin da Mr. Blinken ke neman cimmawa.

Don haka, a yayin da take ganawa da manema labarai tare da Mr.Blinken, ministar harkokin wajen ƙasar Afirka ta kudu Naledi Pandor ta jaddada cewa, ƙasashen Afirka suna da ‘yancin kulla da kuma bunƙasa hulɗa da mabambantan ƙasashe.

Kafofin yaɗa labarai da masana na Afirka ma sun soki sabbin tsare-tsaren ƙasar Amurka a kan Afirka, ganin yadda take yin amfani da ƙasashen Afirka wajen yin takara da manyan ƙasashe, a maimakon kawo wata moriya ga kasashen Afirka.

Sun kuma yi nuni da cewa, “sabon cacar baka” wani tarko ne da kafofin yada labarai na ƙasashen yamma suke yunƙurin danawa, amma ƙasashen Afirka ba sa so su zaɓi wani matsayin da za su dauka ba.

A hakika, ƙasashen duniya na zaman cuɗe-ni-in-cuɗe-ka ne, kuma makomarsu ɗaya ce.

Sai dai abin bakin ciki shi ne, Amurka wadda ra’ayin babakere da nuna fin ƙarfi ya zame mata jiki, ta fi karkata ne kawai ga takara a wannan duniya, a maimakon haɗin gwiwar cin moriyar juna.

Saboda haka, Amurka ta ƙasa fahimtar irin zumunta da haɗin gwiwa da ke tsakanin Sin da Afirka, kasancewarsu ƙasashe masu tasowa ne duka, baya ga manufar makomar bai ɗaya ga dukkanin ‘yan Adam da ƙasar Sin ta gabatar.

A yayin ziyararsa Nijeriya a farkon shekarar bara, ministan harkokin wajen ƙasar Sin Wang Yi ya yi nuni da cewa, Afirka wani babban dandalin haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa ne ba fagen takara tsakanin manyan ƙasashe ba. Alƙawari ne da kasar Sin ta dauka, kuma ƙasar ta cika.

Duk da zancen “barazanar ƙasar Sin” da Amurka ke ƙoƙarin yayatawa, ba za a iya kawar da kai daga nasarorin da ƙasashen Sin da Afirka suka cimma a hadin gwiwarsu ba.

Hanyoyin jirgin ƙasa, da titunan mota, da tashoshin jiragen ruwa, da manyan gine-ginen da ƙasar Sin ta taimaka wajen ginawa a Afirka, duk suna nan a zahiri, waɗanda kuma suke amfanar al’ummun ƙasashen a zahiri.

Ƙasashen Afirka ba sa buƙatar aminiya wadda za ta rika jirkita gaskiya, kuma idanun ‘yan Afirka a bude suke.

In dai da gaske Amurka tana son taimakawa nahiyar Afirka, ya dace ta dauki matakan zahiri, maimakon ta yi amfani da manyan tsare-tsarenta kan nahiyar Afirka, don hana ci gaban haɗin-gwiwar Afirka da wasu ƙasashe.

Mai zane: Mustapha Bulama