Ku daina ziyarar alƙalai cikin dare, inji Alƙalin Kotun Ƙoli

Daga AMINA YUSUF ALI

Alƙalin Kotun Ƙolin Nijeriya, Mai Shari’a Inyang Okoro, ya bayyana cewa, Sashen Shari’a na ƙasar nan ba za ta taɓa yin aikinta yadda ya kamata ba har sai ta tsira daga matsalar tauye haƙƙi daga gwamnatocin jihohi. Wanda ya haɗa da kai ziyara zuwa gidajen alƙalai domin ƙara wa miyarsu gishiri. 

Okoro ya bayyana haka ranar Juma’a a garin Abuja yayin taron laccar da ƙungiyar ma’aikatan Shari’a ta Nijeriya (NBA) ta shirya mai taken: ‘Tauye ikon sashen Shari’a a mulkin demokraɗiyya: Dalilansa, sakamakonsa, da kuma mafita’.

Mai Shari’ar ya ƙara da cewa, in dai wannan ta’adar ta tauye sashen Shari’a ya ci gaba ba tare an yi masa burki ba, ƙasar za ta shiga cikin halin ruɗani. 

Kuma mafitar da za a samu domin a tabbatar da cewa shi ma sashen Shari’a yana samu ya dinga cin gashin kansa ba tare da tsoro ko ko alfarma ba a matsayinsa na sashen mulki mai zaman kansa shi ne, Jami’an gwamnati kada su sake su ziyarci alƙalai a gidajensu cikin dare domin su nemi alfarma.

Sannan kotunan ƙasar nan su tsira daga duk wani matsalolin da ake kawo musu daga waje yayin gudanar da ayyukansu, sannan a daina yin barazana da wulaƙanta alƙalai idan suka ƙi biye wa son zuciyoyinsu. 

Shi ma a nasa jawabin, shugaban ƙungiyar lauyoyi (NBA), Olumide Akpata, ya ce wannan gangami suna yinsa ne don yaƙi da ta tauye talaka don tabbatar da ya samu adalci, sannan da yaƙi da yin dabara da kuma barazana ga lauyoyi.

Inda ya bayyana misali da yadda ka kai wa tsohuwar alƙaliya Mary Odili, hari a gidanta, da dogon yakin aikin ASUU Da sauran abubuwa kamar ɗaure mutane ba bisa ƙa’ida ba, cin zarafin mutane, har ma da ma’aikatan Shari’a da jami’an tsaro suke yi. 

Wannan lacca ta zo kwanaki kaɗan ba bayan mai Shari’a Rabi Gwandu ta kotun masana’antu ta koka da yadda ƙungiyar ‘yan kasuwaa (TUC) ta bijire wa umarnin da ta bayar a kotu, inda Kotun a ƙarƙashin Rabi Gwandu ta da umarnin su ɗage taron da suka yi nufin yi har sai an ji abinda kotun za ta yanke.

Amma wannan bai hana ƙungiyar gudanar da taron nata ba a ranakun 19 da 20 ga Yulin 2022. Duk kuwa da barazanar da kotun ta yi kada a qi bin umarnin ta. 

Kodayake, ƙungiyar ta TUC ta bayyana cewa, ita ma ta samu damar lasisin gudanar da taronta ne daga wani Alƙalin daban wato mai Shari’a O.A Obaseki Osaghae shi ma alƙalin kotun masana’antun ne ta ƙasa.