Ma’aikatu da hukumomin gwamnati sun tsaya cak sakamakon rashin sakin kasafin 2022

Daga AMINA YUSUF ALI

A yanzu haka dai ma’aikatu, sassa da kuma hukumomin gwamnati (MDA) da kuma kamfanonin gine-gine da sauransu sun shiga matsanancin ƙarancin kuɗi a sakamakon jinkirin sakin kasafin kuɗi na shekarar 2022 da ya sa maiakatun suka tsaya cak suka kasa gudanar da manyan ayyukan raya ƙasa. 

A yanzu haka Ma’aikatun da sassa da kuma hukumomin gwamnati (MDA) waɗanda su ne suka fi buƙatuwa da a saki waɗancan kuɗaɗe na kasafin wanda aka ware domin ayyukan raya ƙasa sayen kayan aiki, da sauransu, sun shiga guna-guni a kan jinkirin da aka samu na qin sakin kuɗaɗen bayan cikar wa’adin watanni biyu da ƙarewar tsohon kasafin kuɗin shekarar bara ta 2021.

A cikin kasafin kuɗin na shekarar 2022 Naira Tiriliyan 5.4 aka kasafta a matsayin Kuɗaɗen da za a yi manyan ayyuka da su. Wato su ne suka lashe kaso 34% na jimillar kasafin. Sannan an samu banbanci da kaso da aka ware musu a kasafin 2021. Wato an samu ƙarin kaso 18%.

Ware kuɗin manyan ayyukan yana da matukar muhimmanci don inganta tattalin arzikin ƙasa da kuma gina mutanen ƙasar. 

Wannan jinkirin ya saɓa wa tanadin sashe na 318 na kundin tsarin mulkin ƙasar nan da ya sanya dokar wa’adin kowanne kasafin kuɗin ya ƙare bayan watanni 12. Wato daga ɗaya ga watan Janairu zuwa 31 ga watan Disambar shekarar 2021. 

Amma wannan shekarar bayan kasafin ya ƙare a watan Janairu, sai aka tura shi zuwa watan Maris sannan aka sake tura shi zuwa Afrilu, har ma watan Mayu. A taƙaice ma dai wa’adin ya riga ya wuce tun watanni biyu baya.
 
A binciken da wakilin Blueprint ya yi, ya nuna cewa, ma’aikatun da suka fi jin jiki saboda rashin sakin kuɗaɗen aikin su ne, ma’aikatar gidaje da ayyuka, tsaro, wutar lantarki, musamman ma hukumomin samar da haraji kamar Hukumar Kwastam, hukumar shige da fice, jiragen ƙasa, noma, da sauransu. 

Hakazalika, matsalar rashin tsaro da ta’addanci ita ma tana ƙara samun naƙasu wajen magance ta sanadiyyar rashin sakin waɗancan kuɗaɗe. 

A yanzu haka ma bincike ya nuna cewa, fiye da ayyuka guda 300 ba za su samu yiwuwa ba a sanadiyyar rashin kuɗin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *