Badaƙalar kuɗi: Gwamna Atiku na fafutukar sasantawa da Amurka a bayan fage

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi Sanata Atiku Bagudu ya roƙi Gwamnatin Ƙasar Amurka da ta yi wa Allah ta bari a sasanta zargin badaƙalar Dalar Amurka milliyan ɗari da arba’in ($140,000,000:00), wanda ya yi daidai da Naira Billiyan Hamsin da Takwas da ɗigo Uku (#58.3b), waɗanda tsohon Shugaban Nijeriya, Marigayi Janar Sani Abacha, ya ƙetare da su zuwa ƙasashen waje, waɗansu masu bincike suka gano da hannun Gwamna Atikun dumu-dumu a ciki.

Kamar yadda Jaridar Premium Times ta ruwaito a shafinta ta ce, shari’ar, wacce ke gudana tsakanin sashen shari’a na Ƙasar Amurka, (US Department of Justice, USDOJ) da Ibrahim Bagudu, wanda ƙani ne ga Atiku Bagudu kuma shi ne ke zaman uwa da makarɓiya da ya mika wata takarda ranar Laraba 3 ga Agusta, 2022, inda ya ke neman a dakatar da shari’ar, wacce yanzu haka ke gudana a Kotun Tarayya da ke zama a Birnin Washington da ke Amurka.

Waɗansu bayanai daga kotun suna nuni da cewa, vangarorin biyu dai sun kusa cimma ƙarshen wannan badaƙalar da ta daɗe tana kwan-gaba-kwan-baya, saboda sun yarda da daidaitawa a bayan fage maimakon a shari’a a gaban kuliya.

Atiku Bagudu dai kafin ya tsunduma cikin siyasa shi ɗan kanzagin tsohon Shugaban Ƙasa Janar Abacha ne da ke karakaina wajen safarar biyon kuɗin Abacha tsakanin Nijeriya da ƙasashen waje kafin rasuwarsa a 1998.

Ana sa ran akwai yiwuwar kai ƙarshen wannan badaƙalar daga 3 ga Agusta zuwa 9 ga Nuwamba, 2022, kamar yadda ɓangarorin biyu suka nema a kotun a gundumar Kolombiya.

Duk da ya ke Mai Shari’a John Bates ya aminta da ƙorafin ɓangarorin ya buƙaci bangarorin biyu da su gabatar wa kotu cikakken bayanin matsayar da aka cimma nan da biyu ga watan Nuwamba na wannan shekarar, wanda shi ne zai bai wa kotun sanar cigaba da sauraron shari’ar ko akasin hakan.

Duk da yake tana da kariyar gurfana a gaban kuliya a matsayin sa na gwamna mai ci a Jihar Kebbi, masu bincike na Ƙasar Amurka sun bankaɗo badaƙalar zargin cin hanci da rashawa da kuma maƙudan kuɗaɗe na tsohon Shugaban Ƙasa Janar Sani Abacha da aka danganta da kamfanonin Atiku Bagudu da ke ƙasashe daban-daban.

Rahotannin sun bayyana cewa Atiku Bagudu shi ne da kaso mafi tsoka a cikin badaƙalar da yawansu ya kai dalar Amurka billiyan uku da milliyan shida ($3.6b) da aka ƙwato tsakanin shekarar 1998 zuwa yau.

Rahotannin sun bayyana cewa hukumar hana aikata manyan laifuka ta ƙasar Ingila UK National Crime Agency (NCA) ta ƙwato zunzurutun kuɗi har Dalar Amurka milliyan ashirin da uku da digo biyar ($23.5) daga hannun Muhammed Abacha da Atiku Bagudu.

Idan dai ba a manta ba, Gwamnatin Amurka na tattaunawa da Atiku Bagudu da ƙaninsa Ibrahim Bagudu haɗi da gwamnatocin Nijeriya da Ingila, kamar yadda bayanai daga kotu suka tabbatar.

A wata yarjejeniya da aka rattaɓa wa hannu ranar 26 ga Oktoba, 2018 wacce kwaskwarima ce ga yarjejeniyar farko da aka yi a shekarar 2003 tsakanin iyalan Bagudu da gwamnatin Nijeriya na yafe masa dukkan zarge-zargen da ake yi masa na taimaka wa tsohon Shugaban Ƙasa Abacha wajen fitar da maƙudan kuɗi ta haramtacciyar hanya.

An kuma sanya wa wata yarjejeniyar hannu ranar 6 ga Satumba, 2019, wacce ta bayar da ƙarin wa’adi kan yarjejeniyar farko da aka yi a 2018, wanda wa’adin ya ƙare daga 30 ga Agusta, 2019, zuwa 28 ga Fabrairu, 2020.

A ƙarƙashin yarjejeniyar dai Gwamnatin Nijeriya ta cimma yarjejeniya da Atiku Bagudu na mayar da Dalar Amurka har milliyan Ɗari da hamsin da bakwai da digo biyar ($157.5m), wanda daga ciki za a bai wa Atiku Bagudu Dala milliyan dari da goma ($110m). Sai dai Gwamnatin Nijeriya ta ƙi aminta da biyan sa waɗannan kuɗaɗen, saboda aikata haka tamkar halasta irin wannan badaƙalar ne.

Da man tun farko Gwamnatin Amurka ta yi fatali da wannan yarjejeniyar da aka sanya wa hannu a shekarar 2018 wanda ta ce yin haka tamkar bayar da kariya ce ga halasta satar dukiyar al’umma da ƙoƙarin rufa-rufa bisa ga shari’ar da ke gaban kotu da kuma umarnin da aka bayar na ƙwace dukiyoyin da ya mallaka ta haramtacciyar hanya.

Yanzu haka dai Sanata Bagudu shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar APC wanda kuma ya yi uwa da makarɓiya wajen ganin Bola Ahmed Tinubu ya zama ɗan takarar Shugaban Ƙasar a ƙarƙashin tutar jam’iyyar a babban zaɓe mai zuwa na 2023.

Har wa yau dai binciken da wannan jaridar ta yi ya bayyana cewa, an taɓa tsare Bagudu na tsawon watanni shida a gidan yarin Jihar Texas kafin yanke masa hukuncin zarcewa da shi wata babbar kotu da ke jihar Jersey, sai kafin a miƙa shi ne ya aminta da amayo zunzurutun kuɗi har dalar Amurka milliyan ɗari da sittin da uku ($163m) domin a mayar wa gwamnatin Nijeriya.

An hannanta shi ga mahukunta a Nijeriya da zummar za a hukunta shi bisa ga laifin zamba cikin aminci da satar dukiyar al’umma, sai dai bayan dawowarsa gida Nijeriya abin ya zama busar kura, saboda mahukunta sun kasa ɗaukar matakin gurfanar da shi a gaban kuliya. 

Sai dai duk ƙoƙarin da wannan jaridar ta yi na jin ta bakin Bagudu ko makusantansa ya faskara, saboda rashin ɗaukar waya.