Hukumomi a Tunisia sun yi watsi da matakin gwamnati na sallamar alƙalai

Hukumomin shari’a a Tunisia sun soke korar da shugaban ƙasar Kais Saied ya yi wa alƙalai kusan 50 a farkon watan Yuni.

Matakin shugaban ƙasa na ranar 1 ga watan Yuni na sallamar alƙalai 57 a ƙasar da ke arewacin Afirka, na zuwa ne bayan ya zargi da dama da cin hanci da rashawa da sauran laifuka.

Matakin nasa, wanda ƙungiyoyin kare hakkin bil-Adama suka kira “babban rauni ga ‘yancin shari’a”, ya haifar da yajin aikin alkalai a faɗin ƙasar.

Hamsin da uku daga cikin waɗanda aka kora ciki har da wasu da ake zargi da neman matan da ba muharramansu ba waɗanda suka shigar da ƙara gaban kotun gudanarwa kan yunƙurin Saied.

Kakakin ma’aikatar shari’a na ƙasar, Imed Ghabri ya ce, an soke korar alƙalai 46 da matakin ya shafa, ya ƙara da cewa, an yi watsi da ƙarar da wasu 7 suka shigar.

Kamar yadda bayanai daga ƙasar ke cewa, biyu daga cikin alƙalan kuma suna jiran yanke hukunci, yayin da wasu biyu kuma ba su ɗaukaka ƙara ba.

Lauyan Kamel Ben Messoud ya ce, waɗanda abin ya shafa za su iya ci gaba da aikinsu da zarar an samu takardar shaidar hukuncin da ɓangaren na shari’a suka yanke.