‘Yan cirani fiye da 50 sun ɓace a tekun Aegean na Italiya bayan tasowa daga Turkiya

Jami’an tsaron gavar tekun Girka sun sanar da ɓacewar ‘yan cirani akalla 50 bayan kifewar kwale-kwalen da su ke ciki a tsakar tekun Aegean, akan hanyarsu ta shiga Italiya.

Jami’an tsaron gaɓar tekun Girka sun sanar da gano kwale-kwalen a gab da tsibirin Karpathos da na Rhodes wanda ya taso daga birnin Antalya da ke kudancin Turkiya, gabanin igiyar ruwa ta kifar da jirgin.

Jami’an agajin da suka yi nasarar ceto ‘yan cirani 29 sun ce jirgin ya taso daga Turkiya ne ɗauke da mutane fiye da 80 kuma ya na kan hanyarsa ta zuwa Italiya gabanin haɗarin inda zuwa yanzu ake laluben mutane fiye da 50.

Aikin ceto ‘yan ciranin da ya gudana bisa umarnin ministan harkokin ruwa Yannis Plakiotakis a cewar jami’an tsaron gaɓar tekun an tafi aikin kai ɗaukin da jirage ruwa 4 sai na jami’an 2 kana jirgin saman Sojin ƙasar guda don laluben ‘yan ciranin.

Kakakin ma’aikatar kula da gaɓar teku ta Italiya Nikoa Kokalas ya ce, jirgin ya kife ne sakamakon wata ƙaƙƙarfar Iska da aka yi mai gudun kilomita 50 a sa’a guda wadda ta haddasa haɗarin.

Mr Kokolas ya ce, galibin ‘yan ciranin basa sanye da rigar kariya daga nutsewa dalili kenan da ya sanya da yawa daga cikinsu nutsewa a cikin tekun.

Ratsawa ta Turkiya zuwa Italiya na matsayin hanya mafi sauƙi ga ‘yan ciranin Afrika da Gabas ta Tsakiya don shiga nahiyar Turai da nufin samun ingantacciyar rayuwa, wanda a kowacce rana ke haddasa asarar rayuka.