Ɓarayi sun shiga Gidan Muhammadu Buhari sun ɗibga wa Gwamna Masari sata

Daga UMAR GARBA a Katsina

Rahotannin da Manhaja ke samu yanzu na nuni da cewa wasu ɓarayi da kawo yanzu ba a san ko su waye ba sun sulala cikin gidan Muhammadu Buhari, wato Gidan Gwamnatin Jihar Katsina, inda ake zargin sun sace maƙudan kuɗaɗe da suka kai har Naira Miliyan 31.

Wannan dai ba shi ba ne karo na farko da aka taɓa tafka sata a gidan gwamnatin, domin kuwa a shekara ta 2020 an sace kuɗin da suka kai Naira Milyan 16 a Ofishin tsohon sakataren gwamnatin jihar lamarin da masana ke ganin cewar wasu daga cikin jami’an gidan gwamnatin ne ke tafka ta’asar saboda gidan gwamnatin shine wurin da ya fi kowa ne wuri tsaro a duk faɗin jihar.

Sai dai daga baya an kama waɗanda ake zargi da satar inda ta tabbata cewar ma’aikatan gidan gwamnatin ne.

Tun daga lokacin ba’a sake tayar da maganar ba sai da aka sake yin satar a karo na biyu.

Jaridar Premium Times ta rawaito cewa an sace Naira Milyan 31 ɗin tun ranar 31 ga Yuli, 2022.

Wata majiya daga fadar gwamnatin da ta buƙaci a sakaya sunanta ta bayyana cewa wasu mutane da ba’a san ko su waye ba sun kutsa ofishin mai kula da kuɗi  na gidan gwamnatin su ka kuma yi awon gaba da kuɗin a cikin buhu.

Satar dai ta afku ne da dare lokacin da mai kula da kuɗin Salisu Batsari ke cikin Ofishin.

Majiyarmu ta bayyana mana cewa akwai yiwuwar a gane varawon da ya sace kuɗin saboda ya shiga ta tagar ginin Ofishin ne kuma akwai kyamarar tsaro ta CCTV a wurin.

Tun bayan samun labaran satar da yammacin jiya Alhamis labarin ya kasance batun tattaunawa a tsakanin al’ummar jihar, musamman a kafafen yaɗa labarai na zamani.